✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

An kashe matashi a kan cacar kwallo

Cacar da masu sha’awar kwallon kafa suke yanka don samun kudi kan sakamakon wasan kwallon kafa da za a fafata a tsakanin kungiyoyi, ta yi…

Cacar da masu sha’awar kwallon kafa suke yanka don samun kudi kan sakamakon wasan kwallon kafa da za a fafata a tsakanin kungiyoyi, ta yi sanadiyyar kisan kai inda akawun shagon cacar Abdul dankano ya kashe wani matashi mai suna Mubarak Hassan Adam a  Unguwar Kuchigoro da ke hanyar filin jirgin sama na Abuja.

Cacar wadda gailibi matasa ke yi suna sayen tikiti ne da ya kama daga Naira 100 zuwa sama, inda wadansum kan yanki tikiti da yawa in suka hakikance kungiya kaza za ta ci kungiya kaza kwallo kaza a rabin lokacin farko ko na biyu. 

Idan aka tashi wasan, wanda ya canki daidai sai ya je a biya shi kudin da aka sanya.

Mubarak Hassan ya rasa ransa ne bayan ya yanki tikitin cacar na Naira 150 inda ya ba da Naira 100, bai bayar da cikon Naira 50 ba. Kuma da aka kammala wasa, sai kintacensa ya yi daidai, inda ya je shagon a ba shi kudin da ya ci, amma sai mai kula da shagon ya ce sai dai su raba kudin da ya ci domin shi akawun ne ya cikata sauran Naira 50 a cacar. 

Wata majiya ta yi zargin cewa hakan ne ya sa suka fara fada, inda Mubarak wanda dan kabilar Igala ne ya doki akawun shagon Abdul dankano dan kabilar Ibira, shi kuma Abdul ya ce sai ya rama.

Majiyar ta ce, bayan kwanaki da aukuwar haka ne, sai Mubarak ya je shagon cacar a ranar Lahadin da ta gabata don ya karbi kudinsa, amma sai aka yi rashin sa’a Abdul ya zaro wuka ya daba wa Mubarak, inda Mubarak din ya ruga zuwa shagon mahaifiyarsa da ke kusa, amma Abdul ya bi shi a guje, ya daga wukar ya sake daba wa Mubarak a gaban jama’a da misalin karfe 9:00  na safe. 

Nan take Mubarak ya yi ta zubar da jini aka dauke shi zuwa asibitin unguwar, inda suka ce abin ya fi karfinsu. Sai aka nufi wani babban asibiti inda ana isa likitoci suka ce ya cika.

Mutanen unguwa suna zargin cewa marigayi Mubarak mafadaci ne, don haka mutane suka rufe shagunansu suka gudu, sannan wanda ya yi kisan ya je dakinsa sauya kaya ya ce abokin zamansa ya bar dakin shi ma zai gudu saboda ya yi kisan kai, kuma ya gudu.

Mahaifin Mubarak, Malam Hassan ya ki yin magana kan kisan dansa kuma ya ki bayar da hotonsa ga wakilinmu da ya nema, inda ya ce ya bar lamarin ga Allah, ya dangana.

Makwabta sun shaidi mahaifin Mubarak da cewa mutumin kirki ne wanda ba ya son rigima, kuma ba ya son yawan fada da dansa ke yi.

 Faruwar lamarin ya DPO din Wuye, CSP Salome Hardy-Jimes ta kai jami’anta Unguwar Karmajiji da Kuchigoro don hana tashin rikici a tsakanin matasan yankin har zuwa shekaranjiya Laraba.

Sarkin Unguwar Kuchigoro Malam Ibrahim Wambi ya ce za su taro ranar Asabar mai zuwa shi da CSP Salome Hardy-Jimes da shugabannin kabilu a fadarsa don karfafa batun zaman lafiya da kira ga iyaye su ja wa ’ya’yansu kunne kan su zama masu bin doka.

Hakimin Karonmajigi Alhaji Yunusa Usman Bako ya hori mutanen gundumarsa da ke makwabtaka da Kuchigoro su zauna lafiya btare da tsare doka, kuma matasa su guji yin fada ko amfani da makami.

 

Lokacin da wakilinmu ya tuntubi Kakakin Rundunar ’Yan sandan Abuja Ajinguri Mamzah kan lamarin ta waya bai amsa kiran da yi masa, kuma bai amsa sakon tes da ya aike masa ba.