Wadansu mutane da ake zargin masu satar itacen girki ne sun kashe wani magidanci mai ’ya’ya 12 a ranar ’Jumaar da ta gabata a gonarsa da ke kusa da Makarantar Informatics a garin Kazaure, Jihar Jigawa, inda daga baya suka kone gawar da sankacen kara.
Magidancin mai suna Alhaji Mu’awiyya Gaguli mai kimanin shekara 55 ya tafi gonar ce a ranar Juma’ar domin fakon masu sace masa itace a gonar amma bai dawo ba, kuma sai ranar Lahadi aka gano gawarsa a gonar ta fara zagwanyewa.
Kawun marigayin Malam Sabi’u Shu’aibu da ke Unguwar Kantudu a Kazaure ya shaida wa Aminiya cewa marigayi Malam Mu’awiyya ya hadu da ajalinsa ne a lokacin da ya je gonarsa saboda barayi sun dame shi da yawan satar itace a gonar.
Ya ce ya je gonar ce da niyyar kama wadanda suke sata itacen a ranar Juma’ar da ta gabata, amma har dare bai dawo ba, shi ne matarsa ta zo ta fada a cikin daren suka je gonar ba su same shi ba, amma sun ga jallon ruwansa da buhunsa. Ya ce washegari sun sake komawa gonar suka sake dubawa amma ba su ganshi ba. “Bayan mun dawo gida ne kuma sai wani makwabcin gonar marigayin ya je gewaya ya ga shi ma an sari itacensa, yana gyarawa saboda a ranar wajen gona uku aka yi satar itace a cikinsu. Kuma akwai alamar da keken shanu barayin itacen suka je, mun yi iyakacin kokarinmu don bin sawun amalanken amma da suka shiga gari sai sawunsa ya bace,” inji shi.
Ya ce wani yaro ne ya zo kusa da gonarsa ya ga gawar shi ne aka sanar da su suna suka je suka gan shi akwai alamun duka a kansa amma babu alamar yanka ko fasa cikinsa da jama’a suka yadawa.
Ya ce yanzu haka ’yan sanda suna ta kokarin gano wadanda suke da hannu. Ya ce a yayin binciken sun ga alamar an yi amfani da hiraminsa aka shake masa wuya.
Ya ce marigayin ya rasu ya bar ’ya’ya 12 da mata daya.
Wata majiya ta shaida wa wakilinmu cewa marigayi Alhaji Mu’awiyya yana tara itace ne a gonarsa kuma an samu labarin wadansu matasa suna yi masa satar itacen shi ne ya je domin ya kama su.
Wadansu kuma sun ce kamata ya yi a tuhumi makwabcin gonarsa da ake kai wa taki da amalanke domin an ga sawun a malanke a gonar.
Da yake amsa tanbayoyin manema labarai Kwamandan Hisba na Shiyyar Kazaure Malam Bello Musa Gada ya ce irin haka ta taba faruwa a yankin, don haka ya roki gwamnati ta sa ido kuma a yi kwakkwaran bincike domin a dakile aukuwar irin wannan lamari a yankin. Ya kuma tabbatar da kashe magidancin da kuma kone gawarsa.
Kakakin Rundunar ’Yan sandan Jihar Jigawa SP Audu Jinjiri ya ce ’yan sanda sun tsinci gawar marigayin a gonarsa kuma ya musanta cewa an farke cikinsa kuma babu yanka kamar yadda wadansu suke fada, amma ya tabbatar da cewa an kone gawarsa kamar yadda baturen ’yan sandan yankin ya sanar da shi ta waya. Ya ce ’yan sanda sun dukufa wajen binciko wadanda suka kashe hi kuma dazarar sun kama su za su gurfanar da su a gaban kotu.