Mahara sun kashe wani likita tare da yin garkuwa da wasu mutane takwas a garin Kwassam da ke Karamar Hukumar Kauru a Jihar Kaduna.
Da yake tabbatar da lamarin, dan majalisar Tarayya na Mazabar Kauru, Hon. Zakari Ahmad Chawai, ya ce ana yawan samun hare-hare kai a kai a mazabun Kwassam da Dawaki da ke Karamar Hukumar ta Kauru.
“Kwanaki hudu da suka wuce ’yan bindiga sun kai hari a wata unguwa da ke cikin mazabar Dawaki inda suka sace wasu mazauna yankin, kuma jiya sun sake kai hari a unguwar Kwassam,” in ji shi.
Ya ce masu garkuwa da mutanen sun kashe mutum daya, sun sace mutane takwas kuma sun tafi da wasu kayayyakin mutane da ba a tantance adadinsu ba.
- An janye dokar hana fita a Kaduna da Zariya
- NAJERIYA A YAU: Dabarun Fara Kananan Sana’o’i A Najeriya
Hon. Chawai ya yi kira ga jami’an tsaro da su kara kokari wajen magance hare-haren da ke yawan faruwa a yankin Kwassam da Dawaki.
Daya daga cikin wadanda aka sacen ya samu tserewa daga hannun masu garkuwa da mutane kuma ya kuma yi nasarar komawa gida lafiya.
Rahotanni sun nuna cewa mazauna yankin suna ci gaba da gudanar da ayyukansu na yau da kullum kamar yadda suka saba bayan kwaranyewar abin.
Sai dai har yanzu babu wani bayani daga masu garkuwar kan batun kudin fansa, kamar yadda wani mazaunin Kwassam ya shaidawa wakilinmu.
Kakakin rundunar ’yan sandan jihar Kaduna ASP Mansir Hassan bai amsa kiran da wakilinmu yayi masa ta waya ba a daidai lokacin rubuta wannan rahoton.