Bayan harin da ya yi ajalin wasu matafiya kimanin 25 ranar Asabar a Jos, babban birnin Jihar Filato, rundunar ’yan sandan Jihar ta sanar da kisan wasu karin mutum bakwai da aka yi a ranar Lahadi.
Aminiya ta ruwaito cewa, wannan sabon harin ya auku ne bayan gwamnatin Jihar ta sanya dokar hana fita ta sa’o’i 24 domin kwantar da tarzoma.
Rundunar ’yan sandan ta ce kashe mutane bakwai da aka yi ranar Lahadi a Karamar Hukumar Jos ta Arewa na da alaka da harin da aka kai ranar Asabar kan matafiya a kewayen hanyar Gada Biu da ke yankin Rukuba na birnin Jos.
Kwamishinan ’yan sandan Jihar, Edward Ebuka ne ya tabbatar da hakan yayin wani taron gaggawa da aka gudanar a Fadar Gwamnatin Jihar a ranar Lahadi da daddare.
Ya ce matakin da gwamnatin jihar ta dauka na sanya dokar hana fita ta awanni 24 a wasu Kananan Hukumomi uku ya takaita yaduwar rikicin a Jos.
A cewar Ebuka, wata sanarwa da mai magana da yawun Gwamnan Jihar Makut Simon Macham ya fitar, an ceto mutane 36 daga harin na ranar Asabar cikin aminci.
Egbuka ya ci gaba da bayanin cewa “maharan bata-gari ne da ke son amfani da wannan lamari don tayar da tarzoma a Jihar kuma wannan ba shi farau ba.
“Ba sai mun ambaci sunan kowa, masu barna ne kawai kuma marasa son zaman lafiya,” a cewarsa.
Ya kuma tabbatar da cewa hukumomin tsaro za su yi iya bakin kokarinsu don ganin sun zakulo masu aikata laifuka da bata garin wadanda dole ne su fuskanci fushin doka.
Kazalika, ya shawarci mazauna da su kiyaye dokar hana fita da kuma kaucewa keta haddi kamar yadda hukumomin tsaro ke shirin aiwatar da umarnin Gwamna kan kiyaye doka da oda.
A daren Lahadin da ta gabata ne Shugabannin hukumomin tsaro a jihar suka yi wa Gwamna Simon Bako Lalong karin haske kan yanayin tsaro a jihar da matakin aiwatar da dokar hana fita da aka kafa a Kananan Hukumomin Jos ta Arewa, Jos ta Kudu da kuma Bassa.
Shugabannin hukumomin tsaro da suka halarci ganawar ta sirri tare da Gwamnan sun hada da Kwamanda rundunar Operation ‘Safe Haven’ daKwamishinan ‘Yan sanda, Kwamandan Sojojin Sama da kuma Daraktan Hukumar DSS na Jiha.