Wasu da ake zargin ’yan fasa-kwauri ne sun kashe wani jami’in Kwastam a Juma’ar da ta gabata a lokacin da suke sintiri a hanyar Sinau zuwa Kenu da ke Igboho cikin Karamar Hukumar Baruteen, Jihar Kwara.
Da yake tabbatar da faruwar lamarin ranar Litinin a Ilorin babban birnin jihar, mai magana da yawun hukumar, Mista Chado Zakari ya ce, tun farko jami’an sun kama buhun shinkafa 40 da jarkokin fetur 30 da aka yi fasa-kwaurinsu aka boye a dajin hanyar Sinau zuwa Kenu.
- Mahara sun kashe mutum 2 sun sace 13 a Sakkwato
- NAJERIYA A YAU: Dalilin da ’Yan Najeriya Ke Wasarere Da Gargadin Hukumar DSS.
Ya ce wadanda ake zargin sun bude wa jami’an wuta ne a daidai lokacin da suke kokarin kwashe kayan da aka gano zuwa ma’ajiyar gwamnati.
Ya kara da cewa, sakamakon musayar wutar da aka yi tsakanin jami’ansu da bata-garin, sun rasa mutum daya sannan uku sun ji rauni wanda a yanzu haka ana ci gaba da yi musu magani.
Zakari ya ce tuni an yi wa marigayin, Mista Saheed Aweda jana’iza kamar yadda Musulunci ya tanadar a mahaifarsa Popogbona da ke Karamar Hukumar Ilorin ta Yamma a jihar.
Ya ce sun soma bincike don kamo bata-garin duk inda suka shiga don su fuskanci hukunci daidai da laifin da suka aikata.