Hukumar Tsaro ta Farin Kaya (NSCDC), ta ce jami’anta bakwai ne suka rasu a bakin aikinsu a cikin shekarar 2021 mai bankwana a Jihar Neja.
Kwamandan NSCDS a Jihar Neja, Haruna Bala Zurmi ne, ya bayyana hakan a yayin tattaunawarsa a manema labarai a ofishin hukumar da ke garin Minna, hedikwatar a jihar.
- Fetur din da ke Neja Delta na ’yan Najeriya ne baki daya —Obasanjo
- Direba ya mutu a cikin tankin tankar mai a Kano
Ya ce rundunarsa ta yi aiki a kan laifuka 1,578 da suka danganci cin amana, haura gidajen mutane, sata, cin zarafi, rikicin fili da bashi.
Har wa yau, ya ce sun yi nasarar kwato kudi fiye da Naira miliyan 56, aka mayar wa masu su a 2021.
Ya ce jimullar badakala 1,428 rundunar ta sasanta daga cikin 1,578 da ta samu, an kai 15 kotu sannan an yanke hukunci a kan takwas daga ciki.