Sojojin Faransa sun kashe Shguaban kungiyar IS a yankin Sahara, Adnan Abu Walid al-Sahrawi.
A ranar Laraba, Shugaban Faransa, Emmanuel Macron, ya sanar da kashe al-Sahrawi a matsayin “babbar nasara” ga dakarun Faransa bayan sun shafe sama da shekara takwas suna yakar masu tsattsauran ra’ayi a yankin na Sahel.
- Jirgin soji ya kashe fararen hula 8 ya jikkata da dama a Yobe
- Yadda kashe Al-Barnawi ka iya karya lagon mahara a Najeriya
Duk da cewa Macron, wanda ya ce “sojin Faronsa sun kashe al-Sahrawi”, bai yi bayani ba game da inda aka kashe shi, amma ayyukan kungiyar sun yi kamari a iyakokin kasashen Mali da Jamhuriyar Nijar.
A baya-bayan nan dai shguaban na Faransa na kokarin kwashe dakarun kasarsa daga yankin na Sahel.
Sahrawi shi ne shugabna ISI a yankin Sahel kuma makayansa sun kai munanan hare-hare da suka yi ajalin dakarun sojin kasashen yankin da dama.
A watan Agustan 2020, shi da kansa ya ba da umarnin kashe ma’aikatan jinkai shida ’yan kasar Faransa tare da direbansu dan Jamhuriyar Nijar.
A 2015 ya bayyana mubaya’arsa ga ISIS, wadda ta amince da shi a matsayin jagoranta a yankin Mali da Nijar daga 2016.