✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

An kashe gwamnan Taliban a wani mummunan hari a Afghanistan

An kashe shi ne a ofishinsa

An kashe Gwamnan yankin Balkh ta Arewa a Afghanistan, Mohammad Dawood Muzammil, a wani hari da aka kai a ofishinsa ranar Alhamis.

Bayanai daga kasar sun ce, Muzammil ya zama babban jami’in gwamnati na farko da aka kashe tun bayan da mulkin kasar ya koma hannun Taliban a 2021.

Kawo yanzu tashe-tashen hankula sun ragu matuka a kasar, sai dai an kashe fitattun masu goyon bayan Taliban da wasunsu a hare-haren da kungiyar IS ta dauki alhakin kaiwa.

’Yan sandan yankin sun ce babu wani cikakken bayani game da harin, kuma babu wanda ya fito ya dauki alhakinsa.

Sai dai mai magana da yawun Taliban, Zabihullah Mujahid, ya wallafa a shafinsa na Twitter cewar, gwamnan ya yi shahada a harin da makiya Islma suka kai.

Ya kara da cewa za a fara bincike ba da bata lokaci ba domin bankado wadanda ke da hannu a harin da kuma dalilin kai harin.