An hallaka dan takarar Sanata Inugu ta Gabas a Jam’iyyar LP, Mista Oyibo Chukwu da wasu magoya yansa biyar sa’o’i 48 kafin a shiga zaben ranar Asabar.
Tashin-tashina na ci gaba da kamari a yankin Kudu Maso Gabas duk da karatowar babban zaben 2023.
- NAJERIYA A YAU: Yadda Sabon Shiga A Kada Kuri’a Ke Kallon Zaben 2023
- Ana bikin zagayowar ranar kafa kasar Saudiyya
An ruwaito cewa sai da maharan harbe dan takarar, sannan suka kone shi tare sa magoya bayan nasa a cikin mota a yankin Amechi a Karamar Hukumar Awkunanaw yayin da yake dawowa daga yakin neman zabensa.
Dan takarar gwamnan jihar a Jam’iyyar LP, Chijioke Edeoga, ya tabbatar da faruwar harin inda ya ce ana yi wa ’ya’yan jam’iyyarsu barazana saboda yadda suke kara samun kwarin guiwar takara.
Sai dai har yanzu rundunar ’yan sandan jihar ba ta fitar da wata sanarwa a hukumance game da kisan dan takarar ba.
Mahara sun lashi takobin hana yin zabe a yankin amma jami’an tsaro sun bayar da tabbacin bayar da tsaron da ya dace don gudanar da zaben 2023.