✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

An kashe dan sanda a rikicinsu da sojoji a Adamawa

Kwamishinan ’yan sandna jihar ya bayar da umarnin gudanar da bincike kan lamarin.

Rikicin da ya barke tsakanin ’yan sanda da sojoji a daren Talata ya yi sanadin mutuwar wani Sufeton dan sanda, Jacob Daniel a Jihar Adamawa.

Kwamishinan ’yan sandan Jihar Adamawa, Afolabi Babatola ne, ya yi kakkausar suka kan rikicin da aka yi a mahadar ’yan sanda da ke Karamar Hukumar Yola ta Arewa a baya-bayan nan.

Kwamishinan ya bayyana hakan ga manema labarai da safiyar Laraba cewa lamarin ya yi sanadin musayar wuta tsakanin ’yan sanda da wasu sojoji, wanda ya kai ga mutuwar Sufeto Jacob Daniel.

Ya kuma ba da umarnin gudanar da bincike domin tabbatar da adalci da samun zaman lafiya, yana mai jaddada kudirin rundunar na kare rayuka da dukiyoyin al’ummar jihar.

Kwamishinan ‘yan sandan ya yi bukaci a kwantar da hankali, sannan “An kuma bayyana muhimmancin hadin gwiwa tsakanin hukumomin tsaro wajen kare hakkin jami’an tsaro, wanda zai ba su damar sauke nauyin da ya rataya a wuyansu na yi wa jama’a hidima da kuma kare su.”

 

Ya kuma tabbatar wa jama’a cewa, bangarorin biyu na jami’an tsaro na aiki tukuru domin shawo kan lamarin ta hanyar doka da oda.

Ya kuma yi gargadin cewa daga yanzu ba za a amince da kai hare-hare kan jami’an tsaro da ke bakin aikinsu ba.

“Saboda haka ya zama wajibi dukkanin bangarorin da abin ya shafa su hada kai don hana faruwar irin wannan a nan gaba.”