An kashe wani dan bindiga yayin da suka yi kokarin yin garkuwa da wani dan kasar Indiya a unguwar Dankande, da ke Karamar Hukumar Igabi, Jihar Kaduna.
Jami’an tsaro sun fatattaki ’yan bindigar yayin da suka yi kwanton-bauna da nufin yin garkuwa da bakon a Plan Farm Phase.
- Rashawa: Kotu ta yanke wa Farouk Lawan daurin shekara 7
- ‘Malamai 3,264 ne ke karbar albashin gwamnati suna aiki a makarantun kudi a Kano’
Rundunar ’yan sanda jihar Kaduna ta ce, “A ranar 21 ga Yuni, 2021 da misalin karfe 9:31 na dare, jami’an tsaro da ke rakiyar wani bako zuwa Plan Farm Phase a unguwar Dankande, a Karamar Hukumar Igabi sun yi arba da ’yan bindiga.
“Sun yi musayar wuta da su na wani lokaci amma jami’an sun fatattake su tare da tseratar da dan kasar Indiyar ba tare da wani abu ya same shi ba; A halin yanzu, ’yan bindigar sun gudu zuwa cikin daji tare da raunin harbin bindiga.
“Hadin gwiwar ’yan sanda da sojoji da ke binciken yankin a ranar 22 ga Yuni, 2021 sun gano gawar daya daga cikin ’yan bindigar, bindiga kirar AK47 guda hudu dauke da albarusai 120 da kuma wayar hannu,” inji sanawar da kakakin Rundunar, ASP Muhammad Jalige, ya fitar.
Ya kara da cewar, an ajiye gawar dan bindigar don gudanar da bincike a kanta da kuma wayar hannun da aka samu.
Kwamishinan ’Yan Sandan Jihar Kaduna, CP UM Muri, ya yaba namijin kokarin da suka yi na dakile harin ’yan bindigar.