’Yan fashi sun kashe wani dalibin ajin karshe a Kwalejin Fasaha ta Ibadan, mako guda kafin daurin aurensa.
Kwanan matashin ya kare ne a lokacin da ya ziyarci mahaifiyarsa, a yayin da ake shirin daurin aurensa nasa a ranar Asabar ta makon gobe.
- 2023: Musulmi Bayerabe muke so ya mulki Najeriya
- Matasan Arewa sun yaba wa Buhari kan dakatar da Twitter
Kakakin Kwalejin, Adewole Soladoye, ya ce a ranar Alhamis ne Ebenezer Ayeni, wanda ke zaune a unguwar Bodija a garin Ibadan, ya rasu a unguwar Ojoo na garin, inda mahaifiyar tasa take da zama.
Ya ce a yayin ziyarar da Ebenezer ya kai wa mahaifiyar tasa ne ’yan fashin suka yi wa unguwar dirar mikiya.
Bayan sun kammala aika-aikarsu, sai suka nemi ya yi musu jagora zuwa gidajen makwabatansu, amma ya ki, nan take suka harbe shi a kafa.
An kai shi wani asibiti mai zaman kansa, amma suka ki karbar sa, har ta kai ga ya yi sa’a uku yana zubar da jini, daga baya ya ce ga garinku nan.
Jami’in Hulda da Jama’a na Rundunar ’Yan Sandan Jihar Oyo, Adewale Osifeso, ya tabbatar wa Aminiya da faruwar lamarin a Ibadan.
Adewole Soladoye ya bayyana mutuwar dalibin a matsayin babban rashi ga kwalejin da kuma al’umma, kasancewarsa mai bayar da aikin yi ga jama’a.
Aminiya ta gano cewa marigayin, wanda ke karantan kade-kade a kwalejin, ya dauki mutum fiye da 10 aiki a shagonsa na kade-kade da ke garin na Ibadan.