✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Jami’an tsaro sun kashe dalibai masu zanga-zangar karin kudin makaranta

Daliban Kwalejin Ilimi ta Jihar Kaduna sun yi arangama da jami'an tsaro.

Dalibai biyu ne aka tabbatar jami’an tsaro sun harbe har lahira a yayin zanga-zangar daliban Kwalejin Ilimi ta Jihar Kaduna (KSCOE) da ke Gidan Waya a Karamar Hukumar Jema’a.

Shugaban Kungiyar Dalibai ta Najeriya (NAN), Sunday Asefon, ya tabbatar da samun rahoton mutuwar daliban da kuma wani dalibi da aka harba, daga cikin daliban da ke zanga-zangar kin yarda da karin kudin makarantar da Gwamnatin Jihar Kaduna ta yi musu.

Wani dalibi da ya bukaci a sakaya sunansa ya ce bayan isarsu bakin kofar makarantar a safiyar Litinin, suna ihun ba su da yarda da karin kudin makarantar ba ne suka yi arangama da gamayyar jami’an tsaro.

Dalibin ya ce a nan ne wani daga cikin jami’an tsaron ya yi harbin da ya kashe wani dalibi, sannan aka wuce da dayan don cire masa harsashin da ya same shi.