✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

An kashe dalibai a rikicin manoma a Nasarawa

Rikicin ya barke ne tsakanin manoma ’yan kabilar Alogo da makwabtansu ’yan kabilar Tiv

Ana fargabar rasuwar mutane akalla hudu ciki har da dalibai mata a wani rikicin fili tsakanin manoma a Karamar Hukumar Keana da ke Jihar Nasarawa.

Sabon rikicin ya barke ne tsakanin manoma ’yan kabilar Alogo da makwabtansu ’yan kabilar Tiv a yankin da ke kan iyakar jihohin Nasarawa da Binuwai.

Shugaban kungiyar Mzough U Tiv na Jihar Nasarawa, Philip Nongu, ya ce, “bayanan da muka samu na nuni da cewa cikin mamatan har da daliban Kwalejin Gwamnatin Tarayya da ke Keana, wasu daliban kuma sun makle a dakunan kwananansu.”

Ana zargin rikcin ya samo asaline baya an tsinci gawar wasu ’yan kabilar Alago a gonakinsu a yankin manoman.

Wani ganau da ya nemi a boye sunansa saboda sarkakiyar lamarin ya ce, mutum hudu aka kashe, biyu ’yan kabilar Alago da wasu biyu ’yan kabilar Tiv.

A cewarsa, “Boye muke da iyalaina a wani wuri. Lokacin da na samu bayanai na karshe an kashe rayuka hudu, amma abin ya bazu a cikin gari.

“Kowace kabila an kashe musu mutum biyu wasu da dama sun samu raunuka, kuma a halin yanzu wasu matana na yawo suna wake-wake gami da kada kugen yaki .

“Muna rokon gwamnatin jihar da jami’an tsaro su dauki mataki cikin gaggawa su magance al’amarin.

Shugaban Kungiyar Al’ummar Alago na Kasa (NPAA), Aminu Dan-Elegwu, ya yi Allah-wadai da rikicin musamman a wannan lokaci da jama’a ke fama da matsin rayujwa.

Kakakin gwamnan jihar, Peter Ahemba, shi ma ya la’anci rikicin amma ya ce mutum daya ne ya rasu, wasu hudu sun jikkata.

Amma ya ce shawo kan rikicin kuma jami’an tsaro sun daidata komai a yankin kamar yadda aka saba.

Kungiyar kabilar Tiv a Jihar Nasarawa ta yi tir da rikicin wanda ta ce ya raba manoman kabilar da dama da yankin.

Kakakin ’yan sandan jihar DSP Ramhan Nansel, ya tabbatar da labarin barkewar rikicin, amma ya ce an tura jami’an rundumar domin sawho kansa.

Sai dai ya ce, “rayuka biyu aka rasa wasu mutum biyar kuma suka ji ranuni, amm komai ya dawo yadda yake a baya.