Mako daya bayan ’yan bindiga sun yi garkuwa da shi, rahotanni sun tabbatar da kisan Dagacin garin Madaka da ke Karamar Hukumar Rafi ta Jihar Neja, Zakari Idris.
A ranar Lahadin da ta gabata ne ’yan bindiga kusan su 50 suka yi wa garin kawanya tare da kashe mutum uku da kuma sace basaraken a karo na biyu.
- Mahara sun sace mai gari, sun kone gidaje a Neja
- Mutanen da aka kashe a fadan Hausawa da ’yan kungiyar asiri sun karu
Shugaban Ma’aikatan Shugaban Karamar Hukumar ta Rafi, Mohammed Mohammed shi ne ya tabbatar da kisan a zantawarsa da Aminiya ta wayar salula.
Ya ce tun da farko sai da ’yan bindigar suka tuntubi iyalan marigayin tare da neman N800,000 a matsayin kudin fansa.
Mohammed ya ce mutum biyar da aka sace tare da shi wadanda su suka biya kudin fansarsu sun tabbatar da cewa ’yan bindigar sun kashe basaraken.
A cewarsa, mutanen sun ce ya rasu ne sakamakon irin azabar da ya sha a hannun masu garkuwar saboda irin dukan da suka rika yi masa ba kakkautawa.
Mohammed ya kuma ce ’yan bindigar sun binne gawar mamacin a daji bayan kashe shi.
An sace Mai garin na Madaka ne a karo na biyu kimanin wata daya bayan sako shi, inda a wancan karon ya shafe wata uku a hannun masu garkuwar.
Yayin ba-ta-kashin da aka yi kafin sace Dagacin a ranar Lahadi, an kashe shugaban kato-da-gora na garin, Isyaku Alhassan, dansa, Abdulhamid da kuma wani mutum daya.
Kazalika, an jikkata wasu mutanen da dama tare da kone gidaje masu yawa a garin.