✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

An kashe Ardon Fulani lokacin da yake kokarin ceto

An hallaka wani Ardon Fulani tare da raunata kanensa a wani rikici da ya kaure a tsakanin kabilar Numana da Fulani a kauyen Ninte da…

g Wasu daga cikin ‘yan gudun hijira a rugar HabaseAn hallaka wani Ardon Fulani tare da raunata kanensa a wani rikici da ya kaure a tsakanin kabilar Numana da Fulani a kauyen Ninte da ke gundumar Godo-Godo a karamar Hukumar Jama’a da ke Kudancin Jihar Kaduna.
Rikicin wanda ya faru a yammacin ranar Alhamis zuwa daren Juma’ar makon jiya, ya samo asali ne sakamakon sarar wani dan kabilar Numana mai suna Ango a gonarsa da wani wanda ba a san ko wane ne ba, su kuma ’yan kabilar Numana suka zargi Fulani da aikatawa.
Dagacin garin Ninte, Mista Hassan Jatau Numana ya shaida wa Aminiya cewa: “Bayan na tashi daga gona kafin in dawo gida na yi wanka sai ga wani Fasto ya zo a guje yana shaida wa matasa cewa maza su tashi su shiga daji ga Ango can a gonarsa an sassare shi sosai, nan da nan yaran suka tashi a guje suka shiga daji, ni kuma ganin yadda matasan nan suka yi jerin gwano suka shiga dajin sai na ce ban ga ta zama ba bari in yi maza in kai rahoto. Koda na isa Godo-Godo sai na tarar ofishin ’yan sandan babu kowa zuwa can sai ga matasan sun dauko wanda aka sassara a kan babur suka wuce da shi zuwa asibiti inda likitan garin ya ki karbansa, daga nan sai wani mai suna Zakka ya sa shi a mota na bisu zuwa Babban Asibitin Kafanchan. Bayan mun ijiye shi sai na wuce zuwa babban ofishin ’yan sanda na Kafanchan na shaida musu, su taimake ni ga abin da ke faruwa a garina. Bayan ’yan sanda sun dauke ni a motarsu mun wuce zuwa wata rugar Fulani, koda isarmu sai muka tarar wuta na tashi,” inji shi.
 Dagacin ya ci gaba da cewa, “Da muka karasa ciki sai muka tarar an riga an gama kone komai na Fulanin.
Da Aminiya ta tambaye shi ko akwai wata jikakka ne a tsakaninsu da Fulanin, sai ya ce suna zaman lafiya a tsakaninsu, ba su da matsala ko kadan da Fulanin kuma wannan abin da ya faru ma, zuwa lokacin tattara rahoton, ba zai iya sanin cewa Fulanin ne suka sari mutumin ba.
Yayin da Aminiya ta isa Rugar Habane da ke makwabtaka da garin, inda Fulanin syuke gudun hijira a yanzu wata mai suna Malama Maimuna, ta ce ba su san hawa ba, ba su san sauka ba, bayan wani ya sari dan kabilar Numana a daji ya gudu, “Shi ke nan kawai sai suka biyo mu gidajenmu suna korarmu suna sa wuta mu kuma muna gudu daga nan suka kama Alhaji Ardo Idi (suka kashe shi), mu kuma sai muka gudu daga nan Ninte muka je Nindem muka kwana shi ne washegari aka kwaso mu aka kawo mu nan.”
Ita kuwa Malama Hadiza, yayar marigayi Ardo Idi, uwa daya uba daya, ta ce, “Babu wani abu da ya taba hada mu da su. Wannan karon ma ba mu san hawa ba, ba mu san sauka ba shanu sun dawo kiwo ke nan sai muka hango wani gida gaba da mu can yana cin wuta, sai Alhaji Ardo ya ce kai ga shi can ana kone wa mutumin can gida kuma akwai tsohuwarsa a ciki. Sai ya ce zai je muka yi ta ce masa kada ya je, kada ya je, amma ya kama hanya ya tafi ina ta daga masa hannu cewa kada ka je domin mutanen nan fa za su juyo kanmu ne amma sai ya tafi. Wallahi mu ba mu san abin da ya faru ba.”
Hakimin Godo-Godo Mista Dauda Abanzam, da Aminiya ta same shi a fadarsa, ya tabbatar da cewa ba su da wata matsala da Fulanin da ke wurin da lamarin ya faru, domin zaman lafiyarsu ne ma ya sa shekara biyu da suka wuce, Dagacinsa ya kawo masa marigayi Ardo Idi, ya nada shi sarautar Ardon, kuma ya ce zuwa yanzu ba ya zargin kowa daga cikin Fulanin a kan kisan. Sai dai ya shawarci Fulani makiyaya su daina saurin fushi idan wani abu ya hada su da wani su ce za su sassare shi, kuma su daina tafiya kiwo da makami in ba sanda da aka sansu da ita tuntuni ba.
 Zuwa lokacin hada wannan rahoto komai ya lafa domin an baza ’yan sanda a yankin, sai dai babu wasu harkoki da suke gudana domin duk an watse.
Rundunar ’yan sanda ta tabbatar da mutuwar mutum daya (Ardo Idi) domin su suka kawo gawarsa zuwa dakin adana gawarwaki na asibitin Kafanchan.