✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

An kashe ɗalibai 28, an sace 78 a cikin wata 20

Yankin Kudu kuwa ƙungiyoyin ɗalibai matsafa da fyaɗe da daba su ne matsala a makarantu.

Aƙalla ɗalibai 28 ne aka kashe a yayin da aka 78 sace a manyan makarantun kasar nan a cikin wata 20 kamar yadda bayanan da aka tattara a rahotanni kafafen watsa labarai suka nuna.

Kididdigar wadda ta ƙunshi hare-haren da aka kai wa ɗalibai a makarantu, ba ta haɗa da ɗaliban da aka kashe ko sacewa a kan hanyar mota ba.

Kamar sace ɗalibai 20 da ke karatun kiwon lafiya daga Jami’oin Jos da na Maiduguri da aka yi a Jihar Benuwe kafin daga baya aka sake su.

Kididdigar da aka yi daga watan Janairun 2023 da watan Augustan 2024 ta nuna adadin wadanda aka kashe sun hada da na ayyukan kungiyoyin asiri a jami’o’i da waɗanda aka yi wa fyaɗe da fashi da makami da sauransu a yayin zamansu a makaranta.

Rahotannin sun kuma nuna daliban da suka rasu a sakamakon suka da wuka ko duka ya fi faruwa ne a yankin Arewacin kasar nan kamar Gombe da Nasarawa da Bauchi, inda a Jihar Kwara ne kawai aka samu matsalar ƙungiyoyin ɗalibai matsafa.

Rahotannin sun kuma nuna cewa, a jami’oin da ke Kudancin ƙasar nan an fi samun matsalar ƙungiyoyin asiri na ɗalibai da ke da alyaka da matsafa da suka yi sanadiyar mutuwar dalitbai a jihohi irin su Edo da Osun da Akwa-Ibom da Ogun da Abiya.

Kisan kai ya fi kamari a Kudu a yayin da sace dalibai ya fi a Arewa

Bayanai sun nuna cewa, 28 daga cikin waɗanda aka kashe, 20 sun faru ne a yankin Kudancin ƙasar nan, a yayin da sauran takwas suka faru a jami’o’in Arewa.

Yankin Kudu maso Kudu da Kudu maso Gabas sun fi yawan daliban da aka halaka a cikin makarantu, inda 12 an halaka su ne a Kudu maso Kudu daga cikinsu 10 sun rasu ne a sakamakon rikicin ƙungiyoyin asiri na dalitbai, yayin da dayta an caka masa wuyka ne, dyaya ɗalibar kuma an mata fyaɗe ne har ta mutu.

A manyan makarantun da ke a Kudu maso Yamma kuwa, ɗalibai shida ne suka rasa rayukansu, daga cikinsu huɗu sun rasu ne a sakamakon rikicin da ke da alaƙa da ƙungiyoyin matsafa.

Ɗaya kuma duka aka yi masa har ya rasu, wani kuma an halaka shi aka yi kuma aka binne shi a wani rami.

Amma a Kudu maso Gabas, rahotannin sun nuna yadda ɗalibai biyu suka rasu, inda ɗaya daga cikinsu ya mutu ne a sakamakon rikicin kungiyoyin ɗalibai matsafa, ɗaya kuma ta ɓace ne kafin daga bisani aka tsinci gawarta a cikin makaranta.

A Yankin Arewa kuwa, an fi samun mutuwar ɗalibai a yankin Arewa ta Tsakiya a cikin waɗannan watanni.

Daga cikin ɗalibai shida, huɗu an kashe su a dalilin rikicin ƙungiyoyin ɗalibai matsafa, yayin da sauran biyun kuma masu garkuwa da mutane ne suka kashe su.

A yankin Arewa maso Gabas kuwa, ɗalibai biyu ne, inda wasu masu satar waya suka caka masu wuka, lamarin da ya yi sanadiyar rasuwarsu.

Babu rahotan rikicin kungiyoyin ɗalibai matsafa a yankin Arewa maso Yamma.

Bayanai sun nuna cewa, daga cikin dalibai 78 da aka sace a yankin Arewa ta Tsakiya ne ta yi fice, domin kuwa an sace ɗalibai 42 a makarantu dabandaban a yankin.

Alƙaluma sun nuna an sace dalibai 32 a Jihar Kogi, 7 a Fulato, 2 a Jihar Benuwe sai 1 a Jami’ar Ilorin da ke Jihar Kwara.

Arewa maso Kudu kuwa an samu rahotannin sace mutane ne har sau 29. 24 a Jihar Zamfara, 5 kuma a Katsina.

A yankin Kudu maso Gabas kuwa an samu rahotannin garkuwa da mutane sau 4 kuma duk a cikin Jihar Enugu.

A Kudu maso Kudu, an samu rahotan garkuwa da ɗalibai sau 3 a Jihar Kuros Riba, yayin da makarantu a Kudu maso Gabas ba a samu rohotan garkuwa da ɗalibai ba a cikin watannin.

Ƙungiyar ɗalibai ta buƙaci gwamnati ta ɗauki mataki

Shugaban Ƙungiyar Ɗalibai ta kasa, Mista Lucky Emonefe ya yi Allah-wadai da hare-hare da ake kai wa ɗalibai a makarantun kasar nan.

Mista Emonefe ya bayyana cewa, kungiyarsu ta zauna da Ministan Ilimi, Tahir Mamman a kan yawaitar hare-hare da ake kai wa ɗalibai da garkuwa da su tare da cewa, akwai shirin da ake yi na kafa rundunar samar da tsaro a manyan makarantun ƙasar nan.

Shugaban na ɗaliban ya ce, “a matsayinmu na ƙungiyar ɗalibai, wannan abu dake faruwa ba za mu aminta da shi ba.

“Ba za mu yarda da halaka mana ɗalibai ba haka kurum, musamman halaka dalibai da suka fito neman ilmi.

“A kowace kwaleji dole a samar da shingen jami’an tsaro domin hana yawaitar hare-hare.

“Ba mu san a kai ga har sai mun fito zanga-zanga, amma idan lamarin ya ki ci, ya ki cinyewa dole ne mu yi fito-na-fito, wanda shi ne matakin ƙarshe domin kuwa mun riga mun isar da kokenmu,’’in ji shi.

Shugaban ƙungiyar ɗaliban ya yi kira ga gwamnati a dukkan matakai da su kara tashi tsaye wajen tabbatar da tsaro, musamman a yanzu da makiyan kasa suka mayar da hankalinsu ga manyan makarantu.

Rashin tsaro na neman rugusa tsarin karantarwa — Masana

Wani masanin tsaro a wata ƙungiyar da ke a ƙasar Switzerland, Malam Hafizu Ringim ya bayyana cewa, rashin tsarin tsaro da talauci na daga cikin dalilan da ke ingiza rashin tsaro a makarantunmu a yankin Arewaci da Kudancin ƙasar nan da kuma ƙalubalanta da ake fuskanta.

A Arewa rahotannin fashi da makami da garkuwa da mutane da satar waya da ’yan fashin daji sun zama ruwan dare.

Yankin Kudu kuwa ƙungiyoyin ɗalibai matsafa da fyaɗe da rikicin kungiyoyin daba su ne matsala a makarantu.

“Wadannan matsalolin ne ke za ma matsala ga martabar makarantu tare da za ma barazana ga rayuwar dalibai da malaman makarantun,’’in ji shi.

Ya ƙara bayani da cewa, a yayin da garkuwa da mutane ko dalibai ke da alaka da tattalin arziki a Arewa, saboda karbar kudin fansa, wasu ƙungiyoyin na amfani da shi ne wajen tattaunawa da nufin yin musaya da gwamnati domin jefa tsoro da kawo rashin kwanciyar hankali a yankin.

“A Kudancin Nijeriya dalilin kungiyoyin asiri da fyade da kashe-kashe abu ne da ke da alaka da ayyukan matasa, inda ake jan hankalin daliba5i wajen shiga ko yin rikic,i domin samun kariya daga wasu matasan ko kuma yin koyi da wasu matasan,’’in ji shi.

Alhaji Ringim ya kara da cewa rashin ingantaccen tsari da zai samar da tsaro a jami’o’i da kuma rashin tabbatar da doka da hukunta duk wanda aka samu da laifi ya sa wasu ke shiga cikin harkar da ke kawo rashin tsaro a cikin al’umma.

Ya ce, abin da yin hakan ke kawowa a manyan makarantun kasar nan shi ne raguwar yaran da ke zuwa makaranta, musamman a tsakanin talakawa, wanda hakan ke ƙara giɓin da ke a tsakanin al’umma a fannin karatu da yin kaura zuwa wasu kasashe don neman ilimi.

“Idan ana rage matsalar hare-hare a makarantu ko a kan dalibai dole a dauki tsauraran matakai da za su hada da masu ruwa da tsaki ta kowane fannin da za su fito da hanyoyi da suka dace da kuma yin amfani da fasahohin zamani domin a tabbatar da tsaro a manyan makarantu.

‘Rashin tsayayyun kungiyar dalibai ne ke ta’azzara matsalar tsaro’

Kwa’odinato na Ƙungiyar Kare ’Yancin Ilimi ta kasa, Kwamared Hassan Soweto ya ce, rashin samun tsayayyiyar ƙungiyar matasa a makarantu na daga cikin dalilin da ke sawa a samu rashin tsaro a manyan makarantun kasar nan a tsawon shekaru.

Hassan Soweto ya buga misali da yadda rashin tsaro ya shafi harkar ilimi a yankin Arewa maso Gabas, inda ya kara da cewa, yawaitar hare-hare a kan dalibai alama ce ta nuna gazawa a fannin jami’an tsaro, wanda hakan ya jefa daliban cikin wani mawuyacin hali a bangaren walwala da kuma tsaro.

‘‘Idan aka ci gaba da kai hare-hare ga dalibai ba tare da samar da wani hukunci ba, ilimi zai tabarbare nan da shekara 10 masu zuwa, ba za ka taba samun ilimi da nishadi ba tare da samar da tsaro a makarantu ba.

“Wannan ba wai ya ta’azzara matsalar da ake ciki ba ne, zai shafi batun samar da ilimi ne a kasar baki daya,’’ in ji shi.

Soweto ya kuma yi gargaɗi cewa, dole sai an samu ƙungiyoyin masu cin gashin kansu a makarantun ƙasar nan, sannan kuma shugabanni su magance matsalar tattalin arziki da samar da tsaro, wanda idan ba kuwa ba haka ba, batun kariya ga dalibai abu ne mai wahala.