✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

’Yan Bindiga Sun Kashe Ɗan Kasuwa, Sun Tafi Da Matarsa Da Makwabcinsa A Gusau

Ana fargabar cewa ’yan bindigar sun yi awon gaba da wasu masu sallar Tahajjudi a yankin.

Wasu ‘yan bindiga sun afka gidan wani ɗan kasuwa a birnin Gusau da ke Jihar Zamfara inda suka kashe shi kuma suka yi awon gaba da matarsa da makwabcinsa.

Harin ya faru ne a acikin daren Talata a unguwar Buluku da ke bayan gidan talabijin na Nijeriya (NTA) a Gusau, babban birnin Jihar Zamfara.

Ana kuma fargabar cewa ‘yan bindigar sun yi awon gaba da wasu masu sallar Tahajjudi a wani masallaci da ke yankin.

Wani mazaunin yankin wanda ya buƙaci a sakaya sunansa, ya ce ’yan bindigar sun kashe ɗan kasuwar ne bayan ya ƙi amincewa su tafi da shi.

“’Yan bindigar sun yi yunkurin tafiya da mutumin amma da ya yi turjiya sai suka kashe shi suka tafi da matarsa da makwabcinsa.”

Kwamishinan ‘yan sandan Jihar Zamfara, CP Shehu Muhammad Dalijan, ya tabbatar da kisan dan kasuwar tare da yin garkuwa da mutanen biyu.

Sai dai CP Dalijan ya musanta batun kai wa masallata hari a yankin.

Ya ce “Babu wani hari da aka kai masallaci, abin da ya faru a zahiri shi ne, ‘yan bindigar sun je gidan wani ɗan kasuwa sun yi kokarin tafiya da shi.

“Sai dai bayan ya bijire musu shi ne suka kashe shi, kuma suka yi awon gaba da matarsa da makwabcinsa.”