✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

An kasa gano dan wasan Ghana bayan girgizar kasar Turkiyya

Masaukin dan wasan yana hawa na tara ne a wani otel mai hawa 11, wanda girgizar kasar ta ritsa da shi

Kwana hudu bayan girgirgizar kasa, har yanzu ba a gano inda dan wasan kasar Ghana, Christian Atsu, yake ba, tun bayan da girgizar kasa ta rusa masaukinsa da ke wani bene mai hawa 11 a kasar Turkiyya.

Duk da cewa da farko Kungiyar Kwallon Kafa ta Kasar Ghanta ta sanar cewa an ceto shi da ransa kuma yana asibiti bayan girgizar kasar ta ranar Litinin, amma har yanzu an kasa ganin dan wasan.

Amma Daraktan kungiyar kwallon kafa ta Hatayspor inda Christian Atsu ke taka leda a Turkiyya ya shaida wa kamfanin dillancin labarai na Reuters cewa, “Har yanzu ba mu gan shi ba, duk da cewa an sanar cewa an ceto shi daga baraguzai kuma an kai shi asibiti a ranar Litinin.”

Kafar yada labarai ta Mirror ta ke Birtaniya ta ce masaukin dan wasan yana hawa na tara ne a wani otel mai hawa 11, wanda girgizar kasar ta ritsa da shi, amma ya tsallake rijiya da baya.

Mista Volkan Demirel, ya ce, “Har yanzu babu labarin inda yake, ba wai maganar an ceto shi an kai shi wani wuri ba.”

Ya kara da cewa, ana ci gaba da neman dan wasan mai shekara 31.

Da farko kungiyar kwallon kafar ta sanar cewa, “Mun samu alabrai cewa Christian Atsu an ceto dan wasan daga baraguzan ginin, kuma yana samun kulawa a asibiti; a sanya shi a addu’a.”

Christain Atsu, dan kasar Ghana ya fara wasa a kulob din Hatayspor da ke gasar Super Lig ta kasar Turkiyya ne a watan Satumbar 2022.

Kafin komawarsa, ya yi wasa a kungiyoyin Chelsea, Everton, Bournemouth kuma Newcastle United da ke Birtaniya.