Wata kungiyar matasa mai suna IEYAN reshen Jihar Filato ta karrama wadansu manyan mutane su 11 da ta ce sun bayar da gudunmawa, a bangarori da dama na taimaka wa al’umma a Jihar Filato.
Kungiyar ta gudanar da taron karramawar ce, a ranar Lahadin da ta gabata a garin Jos, babban birnin Jihar Filato.
Mutanen da aka karrama sun hada da Shugaban Kungiyar Masu Sayar da Buhuna ta Jihar Filato Alhaji Iliyasu Muhammad da Daraktan Ayyuka na Karamar Hukumar Jos ta Kudu, Mista Daniel Bot da Alhaji Nafi’u Barikin Ladi da tsohon Shugaban Jam’iyyar PDP ta Karamar Hukumar Jos ta Arewa Alhaji Yaro Mai Rake da Mista Luka Panpe da sauransu.
Da yake jawabi a wajen bikin Shugaban Kungiyar IELAN reshen Jihar Filato, Kwamared Ajiya Wuddeama ya ce sun karrama wadannan mutum 11 ne, kan irin gudunmawar da suke bayarwa wajen taimakawa al’ummar Jihar Filato a bangarori daban-daban domin karfafa musu gwiwa.
Ya ce kamar Shugaban Kungiyar Masu Sayar da Buhu ta Jihar Filato Alhaji Iliyasu Muhammad sun karrama shi ne saboda taimaka wa matasa da yake yi, wajen samar musu da ayyuka a gwamnati da kamfanoni masu zaman kansu.
Ya ce ya samar wa matasa da dama aikin dan sanda da aikin shige da fice da aikin Kwastam da kuma samar wa matasa ayyuka a wurare daban-daban a jihar.
Ya ce a shirye kungiyar take ta ci gaba da zakulo irin wadannan mutane da suke taimaka wa al’umma domin ta karfafa musu gwiwa.
Ya yi kira ga jama’a musamman masu hannu da shuni su rika taimaka wa al’umma.
A jawabin Alhaji Iliyasu Muhammad ya bayyana matukar farin cikinsa da karramawar da wannan kungiya ta yi musu.
“Muna yin wannan aiki ne don Allah ba tare da kowa ya sani ba.
Amma Allah Ya sanar da wannan kungiya cewa ga hidamar da muke yi wa al’umma. Babu shakka duk wanda yake ayyukan alheri, aka nuna an ji dadi zai yi farin ciki, kuma zai samu karfin gwiwa, wajen ci gaba da wadannan ayyuka,” inji shi.