Wata Kwalejin Ilimi a garin Jos mai suna The Green College ta karrama Gwamna Rochas Okorocha na Jihar Imo da tsohon Ministan Sadarwa, Alhaji Ibrahim Dasuki Salihu Nakande da tsohon Kwamandan Rundunar Samar da Zaman Lafiya a Jihar Filato, (OPSH), Manjo Janar Rogers Ibe Nicholas kan gudunmuwar da suke bayarwa wajen samar da zaman lafiya, hadin kan kasa da kuma ci gaban ilimi a Jihar Filato da kasa baki daya.
Sauran mutanen da aka karrama a lokacin da kwalejin take bikin yaye dalibanta a dakin taro na kungiyar SSANU da ke Jami’ar Jos sun hada da Daraktan Hukumar tsaro ta DSS na Jihar Filato, Iro Abdullahi Danmusa da Farfesa Warisu Ayosheni Ali da Daraktar Sashin Kare Hakkin Kwastomomi ta Babban Bankin Najeriya (CBN), Hajiya Khadijah Kassim da kuma Zainab Mu’azu ‘yar shekara 14 da ke yin takalman zamani.
Shugaban Kamfanin Assabikoon Inbestment Ltd, kamfanin da ya kafa Kwalejin, Alhaji Sani Bala ya ce sun karrama Gwamna Rochas ne sakamakon jajircewarsa wajen gina kasa, makarantu a Arewacin kasar nan da kuma burinsa na ganin kasar nan ta samu zaman lafiya.
Ya kara da cewa sun karrama Hajiya Khadija Kassim dalilin jajircewar da ta yi wajen taimaka wa mata don su samu ilimin zamani da na addini, shi kuma Dasuki Nakande dalilin kafa gidan rediyon Unity FM da ya yi fice wajen yada shirye-shirye masu ilimantar da al’umma.
Ita kuwa Zainab Mu’azu mai kimanin shekara 14 sun karrama ta ne sakamakon jajircewar da ta yi wajen yin takalma har ya kasance daga wadansu garuruwa ma ana zuwa sari wurinta, duk da karancin shekarunta.