Hajiyar da tsinci kudi dala 80,000 a Saudiyya, Aisha Nuhuche ta samu kyautar N250,000 saboda rikon gaskiya da amana.
An kuma karrama hajiyar da lambar yabo ta ‘Jakadar Rikon Gaskiya da Amana’ ta gidauniyar T.Y. Burutai.
- Dalilin dawo da hoton Sanusi a dakin taron gidan gwamnatin Kano
- Yadda na yi tsintuwar kusan Naira miliyan 60 ina ɗawafi a Harami — Hajiyar Zamfara
Da yake jawabi yayin mika kyautar kudi da satifiket, shugaban gidauniyar, Ibrahim Dan Fulani ya bayyana Hajiya Aisha a matsayin mace sha yabo da ya kamata a yi koyi da ita.
Ya tunatar da ‘yan Najeriya muhimmancin yin abin da ya dace a ko da yaushe, “Bayan samun kudin Hajiya Aisha ba ta yi kasa a gwiwa ba wajen mayar da kudaden ga Hukumar Alhazai ta Jihar Zamfara, inda daga nan ne aka mayar da kudaden ga hukumomin da abin ya shafa a kasar Saudiyya.”
Ya kara da cewa gidauniyar za ta ci gaba da kokarin kawo sauyi a rayuwar daidaikun mutane.
Daga nan sai ya yi kira ga ‘yan Najeriya da su sanya gaskiya da rikon amana a cikin rayuwarsu ta yau da kullum, da kuma yin zabin da zai yi tasiri ga mutanen da ke tare da su.