✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

An kashe mutane da dama a sabon harin da aka kai Jos

Ana zargin an kashe mutum 30 a sabon harin da aka kona gidaje da dama.

Mutane da dama ne ake fargabar an kashe wani sabon hari da aka kai da tsakar dare a yankin Yelwan Zangam da ke Karamar Hukumar Jos ta Arewa a Jihar Filato.

Wani mazaunin yankin, Yakubu Bagudu, ya tabbatar wa wakilin Aminiya cewa maharan sun kashe sama da mutum 30 farmakin da aka kai a daren ranar Talata zuwa wayewar garin Laraba.

Aminiya ta kuma gano cewa maharan sun kuma kona gidaje da dama a yayin sabon harin.

A lokacin tattaunawarmu da shi, Yakubu ya ce an girke jami’an tsaro a yankin.

Ya zuwa lokacin hada wannan rahoton dai, Rundunar ’Yan Sanda ta Jihar Filato ba ta fitar da wani karin bayani ba a kan harin.

An kai farmakin ne kimanin mako daya bayan an tare an kuma kashe wasu Fulani matafiya kimanin 30 a kan hanyar Gada-Biyu zuwa Rukuba a Karamar Hukumar ta Jos ta Arewa.