✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

An kara sako dalibin Jami’ar Greenfield

Mahaifiyar ta shaida wa Aminiya cewa ’yan bindiga sun sako shi a karshen mako.

’Yan bindiga sun kara sako daya daga cikin daliban Jami’ar Greenfield da ke Jihar Kaduna da ke hannunsu.

Mahaifiyar dalibin da aka sako ta shaida wa Aminiya ’yan bindigar sun sako dan nata ne a karshen mako da ya gabata.

A ranar Talata, mahaifiyar daliban, Laurentia Adamu, ta tabbatar wa Aminiya cewa an sako mata danta, amma ba ta yi karin bayani ko an biya kudin ba.

Hakan na zuwa ne bayan masu garkuwa da daliban sun yi barazakar kashe su muddin ba a ba su kudin fansa Naira miliyan 100 da babura 10 zuwa ranar Talata, 4 ga watan Mayun 2021 ba.

Idan ba a manta ba, ’yan bindigar sun yi garkuwa da dalibai 22 a Jami’ar Greenfield, daga baya suka kashe biyar daga cikin daliban domin nuna wa gwamnati gazawarta kan cika sharudan da suka gindaya.

’Yan bindigar sun fara neman a biya su Naira miliyan 800 a matsayin kudin fansa, inda kwanaki uku bayan wa’adin nasu suka kashe uku daga cikin daliban, kafin daga baya suka kara kashe wasu biyu.

’Yan bindigar sun yi barazanar ci gaba da yi wa daliban kisan dauki dai-dai muddin ba a cika sharudan da suka bayar ba.

Sashen Hausa na muryar Amurka ya ruwaito shugaban ’yan bindigar mai suna Sani Idris Jalingo yana cewa, muddin Gwamnatin Jihar Kaduna da iyayen daliban suka ki biyan kudin fansar tare da kawo musu baburan, kirar Honda guda 10, to za su kashe ragowar daliban da suke hannunsu.

Jalingo ya ce, Iyayen daliban tuni sun biya su Naira miliyan 55 a matsayin kudin fansa.

“Mun ji kalaman Gwamnan Jihar Kaduna cewa ba zai biya ’yan bindiga kudin fansa don kada su samu damar kara siyo wasu makamai ba.

“Ya fada wa iyaye cewa shi ba zai biya kudin fansa ba idan aka yi garkuwa da mutum, don haka, muna so mu nuna gazawar gwamnatin Najeriya shi ya sa muka kashe daliban,” a cewarsa.

Wasu dalibai biyu cikin wadanda aka yi garkuwa da su, wadan da suka yi magana sun bukaci gwamnati da iyayensu da su dauki lamarin da muhimmanci.

Daya daga cikinsu wanda jika ne ga Sarkin Zazzau na 18, Alhaji Shehu Idris, ya yi kira ga gwamnati da ta daidaita da ’yan bindigar.

“Tabbas za su aikata abun da suka fada saboda tuni sun kashe wasu daga cikinmu,” inji dalibin.

Ita ma wata dalibar, Abigail Usman, ta bukaci gwamnati da ta turo kudin fansarsu don su samu su shaki iskar ’yanci.

Ta ce, “an kashe biyar daga cikinmu kuma a kan idonmu aka kashe su.

“Idan har ba su samu kudin ba za su kashe mu gaba dayanmu,” inji ta.

A ranar 20 ga Afrilu, 2021, ’yan bindigar suka shiga jami’ar bayan sun yi wa mai gadin Jami’ar kisan gilla.

Aminiya ta ruwaito Gwamna Nasir El-Rufai ya yi watsi da tattaunawa ko biyan ’yan bindigar kudaden fansa domin su sako daliban.