Kamfanin rarraba wutar lantarki na Kaduna Electric ya kara kudin kowane kilowatt zuwa N209.
Kaduna Electric ya sanar a safiyar Laraba cewa karin kudin wutar ya shafi kwastomomin da ke amfani da layin Band A ne kawai.
Sanarwar mai dauke da sa hannun kakakin kamfanin, Abdulazeez Abdullahi, ta ce karin kudin ya fara aiki tun ranar 1 ga watan Yuli da muke ciki.
Karin kudin daga N206 zuwa N209 dai na zuwa ne kimanin wata guda bayan rage shi, sakamakon caccaka da kamfanonin rarraba wutar lantarki a Najeriya suka sha bayan sun kara kudin saboda Gwamnatin Tarayya ta janye tallafi a bangaren.
A kwanan baya kamfanonin suka rage karin bayan sanya baki da majalisar dokoki ta kasa ta yi.
Ana iya tuna cewa majalisar dokokin Najeriya ta yi soki tsarin da kamfanonin rarraba wutar lantarki suka bullo da shi na raba masu amfani da wutar zuwa rukunin Band A, B,C da kuma Band D.
Band A shi ne layin da kamfanonin suka ba kwastomomin da ke amfani da shi tabbacin samun wutar lantarki ta akalla awa 20 a kowace rana.
Sauran layukan kuma ba su da wannan tabbacin.
Sanata Ali Muhammad Ndume ya bayyana cewa wannan bambanci da kamfanonin suka kirkiro ya ci karo da kundin tsarin mulkin Najeriya, wanda ya wajabta daidaita tsakanin ’yan kasa.