Jihar Nasarwa ta kara tsawon hutun jego ga ma’aikatanta mata daga wata hudu zuwa shida domin su samu damar shayar da jariransu nonan uwa.
Kwamishinan Lafiya na Jihar Nasarawa, Ahmed Baba Yahaya ya bayyana hakan yayin karbar bakuncin kungiyar rajin amfani da abinci mai gina jiki a Najeriya (CS-SUNN), a rangadin da ta ke yi kan muhimmancin shayar da yara nonan uwa a kwana 1,000 farko na rayuwarsu.
- Sarkin Saudiyya ya tattauna da Buhari
- Shugaban karamar hukuma ya yi wa mai neman kujerarsa dukan kawo-wuka
- Hadimin Ganduje ya gwangwaje matasa da tallafin Jakuna
Ahmad Baba, ya ce karin wa’adin hutun haihuwar da gwamnatin ta yi wa ma’aikatanta mata wani tagomashi ta fuskar gina rayuwar dan Adam.
Ya yi albishir cewa, nan gaba gwamnati za ta aike da kurin karin hutun ga majalisar dokikn jihar don mayar da shi doka a fadin jihar.
“Za mu yi kokarin samar da kariya da kula da lafiyar yara da inganta rayuwarsu ta yadda yara masu tasowa za su zama masu fikira da fasahar kirkire-kirkire da za su bayar da gudunmawa wurin cigaban jiharsu da kasa baki daya”, inji shi.
Ya ce gwamnatin jihar na maraba da kungiyoyi masu rajin wayar da kan jama’a kan muhimmancin shayar da nonon uwa.
A nata bayanin, shugabar CS-SUNN a Jihar Nasarawa, Mercy, ta ce karin hutun haihuwar zai taimaka wa iyayen yara su kara murmurewa bayan sun gama shayarwa kuma ba su da fargabar yiyuwar rasa damarsu ta aiki.