✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

An kara farashin man fetur ta bayan fage —IPMAN

Ana zargin masu manyan rumbunan ajiyar mai da yin haka don samun kazamar riba.

Kungiyar Dillalan Man Fetur ta Kasa (IPMAN) ta zargi masu wuraren ajiyar mai da kara farashin man ta bayan fage da kuma neman kirkiro wahalar mai na karya domin su samu kazamar riba.

Shugaban kungiyar IPMAN Reshen Jihar Kano, Bashir Danmalam, ya yi zargin cewa tun ranar Juma’ar da ta gabata masu manyan rumbunan mai da ke Legas da Warri da Kalaba suka kara farashin litar mai daga N148 zuwa tsakanin N153 da N155, domin kawo rudani.

“IPMAN na zargin manyan masu rumbunan mai da yi wa Gwamnatin Tarayya zagon kasa ta hanyar yin gaban kansu wajen kara farashin mai duk da cewa gwamnati ba ta kara farashi ba.

“Muna rokon kamfanin NNPC ya gaggauta gudanar da bincike, saboda tun rana Juma’ar makon jiya wadansu suka kara farashin daga N148 suka mayar N153 zuwa N155 kowace lita.

“Sanin kowa ne cewa Gwamnatin Tarayya ce kadai take shigo da mai ba ’yan kasuwa ba,” inji sanarwar da ya fitar a Kano ranar Juma’a.

Bashir Danmalam ya kuma zargi masu wuraren ajiyar man da neman kirkiro da matsalar karancin mai domin su samu kazamar riba saboda sun ga karshen shekara na kara matsowa.

Ya ce tona musu asiri yana da muhimmanci domin ankarar da gwamnati ta dauki mataki, saboda kar a dora wa kungiyar IPMAN laifin da ba nata ba idan aka wayi gari gidajen mai sun kara farashin litar mai.