Shugaban Karamar Hukumar Lere da ke Jihar Kaduna Alhaji Abubakar Buba, ya ce Gwamnan Jihar Malam Nasiru El-Rufa’i ya fara biyan mafi karin kashi 30 na albashi ga ma’aikatan jihar ne don kyautata rayuwar ma’aikatan.
Alhaji Abubakar Buba ya bayyana haka ne lokacin da yake jawabi ga ma’aikatan Karamar Hukumar Lere lokacin da suka kawo masa ziyarar mika godiya kan karin albashi da aka yi musu, a karamar hukumar.
Ya ce don haka lokacin da sauran gwamnonin kasar nan suka tsaya suna tunani kan yiwuwar wannan karin albashi, sai kawai aka ji Gwamna El-Rufa’i ya yi karin, kuma ya fara aiwatar da shi nan take.
Ya ce don haka su ma ya zamo musu wajibi su yi karin albashin a dukkan kananan hukumomin jihar.
“Wannan abu da Gwamnatin Jihar Kaduna ta yi ya zama wajibi ga ma’aikatan Jihar Kaduna, kowa ya tsaya ya yi aikinsa tsakani da Allah. Don haka muna kira ga ma’aikatan su rika zuwa aiki a kan lokaci, kuma su rika kaiwa har lokacin tashi. Yanzu gwamnati ba za ta amince da zuwa aiki a makare ko rashin zuwa wajen aiki ba. Domin ba zai yiwu gwamnati ta dadada wa ma’aikata, su kuma su ki yin ayyukan da aka dauke su ba,” inji shi.
Ya yi kira ga ma’aikatan su tsara rayuwarsu kan wannan karin albashi, kada su yi albazaranci. Su yi abubuwan da za su taimaki rayuwarsu.
Tun da farko a jawabin Shugaban Kungiyar Ma’aikatan Kananan Hukumomi ta Najeriya (NULGE), Reshen Karamar Hukumar Lere, Kwamared Lawal Abubakar ya ce sun zo ne domin su mika godiyarsu ga Shugaban Karamar Hukumar ya kai ga Gwamnan Jihar Kaduna, Malam Nasiru El-Rufa’i kan wannan karin albashi da aka yi musu.
Ya ce babu shakka wannan karin albashi ya inganta rayuwar ma’aikata, musamman na Karamar Hukumar Lere. Domin tunda aka fara biyan karin albashin ma’aikatan suka shiga cikin farin ciki da annashuwa.