A ranar Lahadin da ta gabata ce aka kammala musabakar karatun Alkur’ani Mai girma na Karamar Hukumar Jama’a da aka gudanar a garin Kafanchan.
Lokacin da yake bayani a wajen rufe musabakar, Mataimakin Shugaban Kwamitin Musabaka na Jihar Kaduna, Alhaji Tasi’u Sulaiman, Talban Kachia ya yi kira ga dalibai masu musabaka a Karamar Hukumar Jama’a su yi kokari wajen dawo da martabar da aka sansu da ita a fagen musabaka a shekarun baya.
Talban Kachia wanda ya wakilci Shugaban Kwamitin Musabaka na Jihar Kaduna, Dokta Bello Abdulkadir, Salanken Zazzau, ya jawo hankalin malaman makarantun allo da na Islamiyya kan su kara juriya kan yi wa Alkur’ani hidima inda ya ce sakamakonsu yana wurin Allah Mai girma.
Sannan ya gargadi dalibai musamman masu haddar Kur’ani su rage yawan kallace-kallacen fina-finai da wakoki saboda hadda.
Ya kuma yi kira ga masu haddar Kur’ani da su lizimci halayen kwarai tare da kyautata dabi’unsu don gudun bata sunan Musulunci da Musulmi a idon makiya.
“Shi hadda ba ya zama a zuciyar fasiki mai yawan sabon Allah,” inji shi
Da yake gabatar da nasiha kan muhimmancin Alkur’ani, Dokta Habib Tijjani Tahir ya jawo hankalin al’ummar Musulmi su tashi tsaye wajen koyon karatun Alkur’ani da haddarsa da fahimtar sakonsa da kuma yin aiki da shi, wanda shi ne manufar aiko Manzon Allah (SAW) da shi ga duniya.
A karshe ya jawo hankalin masu shiga musabaka kan su rika yin komai saboda Allah. “Kada ya zama manufarka kawai ita ce a ce ka fi kowa iya karatun Alkur’ani ko ka fi kowa murya ko kana yi ne don a yaba maka ko don wani abin duniya da za a ba ka wanda ba shi ne hadafi ba, musabaka hanya ce ta cusa kaunar koyo da haddar Kur’ani don haka kada ku mayar da ita hadafin karshe,” inji shi.
Da yake tofa albarkacin bakinsa, Mai martaba Sarkin Jama’a Alhaji Muhammad Isa Muhammad wanda Sarkin Gandun Jama’a Alhaji Suleiman Isa ya wakilta, ya mika godiya ga kwamitin da suka dauki nauyin shirya gasar tare da kammala shi lafiya.
Sarkin, ya kuma yi kira ga kwamitin ya ci gaba da rike wannan muhimmin aikin na taimaka wa dalibai wajen koyon karatun Alkur’ani Mai girma da kuma haddarsa.
da yake bayyana sakamakon gasar, jagoran alkalan musabakar, Malam Zakariyya Kachia ya bayyana godiyarsa da irin hadin kan da ya samu tun daga ’yan kwamitin har zuwa kan daliban da suka gabatar da karatuttuka.
A karshe ya bayyana wadanda suka yi nasara a dukkan matakai shida da suka kunshi Izifi biyu zuwa Izifi sittin, inda aka bayyana Ja’afar Zakariyya a matsayin ‘Gwarzon Shekara’ na karamar hukumar bayan ya zo na daya a matakin Izu sittin.