An kammala jana’izar Sarkin Zazzau, Alhaji Shehu Idris bayan rasuwarsa a ranar Lahadi.
Wakilin Aminiya ya ce an kammala Sallar Jana’izar sarkin ne da misalin 5:35 na yamma.
Dubun dubatar jama’a daga sassan Najeriya sun halarci sallarci jana’izar da suka hada da manyan jami’an gwamnati, sarakuna, attajirai da fitattun mutane.
Ratotanni sun ce an gudanar da jana’izar ce a cikin gida saboda yawan malarta jana’izar suka cika wajen fadar sarkin.