✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

An kammala gasar cin Kofin AHLAN a Kano

Ranar Larabar da ta gabata ce aka kammala gasar cin Kofin AHLAN da Hukumar Kwallon Kafa (FA) ta Jihar Kano ta shirya. Shugaban Hukumar FA, …

Ranar Larabar da ta gabata ce aka kammala gasar cin Kofin AHLAN da Hukumar Kwallon Kafa (FA) ta Jihar Kano ta shirya. Shugaban Hukumar FA,  Rabi’u Inuwa Ahlan ne yake daukar nauyin shirya gasar a tsakanin manya kungiyoyin kwallon kafa na kasa a duk karshen kakar wasanni kafin a fara wasannin sabuwar kaka.

A bana manyan kungiyoyin kwallon kafa 12 ne suka fafata a birnin Kano. Kungiyoyin sun hada da Enyimba United da Kano Pillars da Katsina United da Kwana United da Plateau United da Jigawa Golden Stars da sauransu.  Kungiyar kwallon kafa ta Plateau United ita ce ta zama zakara ta dauki kofin bayan da ta doke abokiyar karawarta El-Kanemi Warriors ta Maiduguri da ci 1-0 a wasan karshe a filin wasa na Sani Abacha da ke Kofar mata a birni Kano.

Sai kuma kungiyar kwallon kafa ta Jigawa Golden Stars ta zo ta uku bayan da ta lallasa a abokiyar karawarta wato kungiyar kwallon kafa ta Rarara da ci 4-1. Manyan bakin da suka halarci wasan karshen sun hada da Shugaban Hukumar Shirya Gasar Rukuni-Rukuni ta kasa, Malam Shehu Dikko.