✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

An kame mutum biyar da suka kai hari ofishin ’yan sanda a Imo

An taba kone ofishin 'yan sandan a lokacin zanga-zangar EndSARS a shekarar 2020.

’Yan sanda a Jihar Imo sun tabbatar da cafke mutum biyar daga cikin maharan da suka yi yunkurin kone ofishin ’yan sanda na Orji a Jihar.

Kakakin ’Yan Sandan Jihar, SP Bala Elkana, ya tabbatar da hakan cikin wata sanarwar da rundunar ta fitar a ranar Talata.

A cewarsa, an kame maharan ne da suka yi yunkurin kone caji ofis din Orji, wadda aka taba konawa a lokacin zanga-zangar EndSARS a shekarar 2020.

Ya ce, “Sun ajiye motarsu a bayan gari yayin da suke kokarin kone caji ofis din, amma da wata tawagar jami’anmu suka tunkare su bisa jagorancin Kwamishinan ’Yan Sanda CP Abutu Yaro, sai suka tsere.

“Gaba daya an rufe yankin, kuma an yi nasarar kame mutum biyar daga cikin wanda suka yi yunkurin kai hari.

“Yanzu haka ana fadada bincike don kama ragowar da suka tsere da makamansu”, a cewar Elkana.