✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

An kama ɗan bindiga mai shekara 70 a Kaduna

An kama ƙasurguman huɗu da suka addabi mazauna yankin Arewa maso Yamma.

Rundunar ’Yan Sandan Jihar Kaduna, ta cafke wani tsoho mai shekara 70 da ake zargin ɗan bindiga ne a Zariya.

Rundunar ta kama dattijon ne tare da wasu mutum uku.

Wanda ake zargin, ɗan unguwar Tudun Jukun a garin Zariya, jami’an tsaro sun cafke shi, biyo bayan wasu bayanan sirri da suka samu a kansa.

Kakakin rundunar jihar, Mansir Hassan, ya ce an ƙwato bindiga ƙirar AK-47 da bindigar gida da harsashi guda uku daga hannun wanda ake zargin.

“Bayan bayanan sirri da suka samu game da yunƙurin wani ɗan bindiga da ake zargi, ’yan sanda a yankin sun kama mutumin mai shekara 70 a duniya, daga Tudun Jukun a Zariya.

“An kama su ne da misalin ƙarfe 2:50 ma rana. A yayin samamen, an ƙwato bindiga ƙirar AK-47, bindigar gida, da harsashi guda uku daga hannun wanda ake zargin.

“Ɗaya daaga cikin waɗanda aka kama yana taimaka wa binciken ’yan sanda, kuma za a gurfanar da shi a gaban kotu da zarar an kammala bincike.”

Ana zargin mutanen da kai hare-hare a wasu yankunan Arewa maso Yamma.

Kakakin rundunar, ya ce waɗanda ake zargin sun yi garkuwa da mutane da dama da satar shanu.

Ya ce sun shiga hannu ne ta hanyar haɗin gwiwa da rundunar ’yan sanda daga Saminaka da mafarauta a Ƙaramar hukumar Lere ta Jihar Kaduna.