Dubun wani ɗan bindiga ta cika a yayin da yake shirin shiga jirgi tare da sauran maniyyata aikin Hajji a Jihar Sakkwato.
Jami’an hukumar tsaro ta DSS sun kama ɗan ta’addan mai suna Sani Galadi ne a yayin da ake yi wa maniyyata tantancewar ƙarshe kafin hawa jirgi zuwa Ƙasa Mai Tsarki a Filin Jirgi na Sultan Abubakar da ke jihar.
An kama shi ne a safiyar ranar Litinin, washegarin da jami’an tsaro suka kama wani ɗan bindiga yana yana shirin hawa mota zuwa filin jirgin sama na Abuja domin zuwa aikin Hajji.
Ɗan bindigar da aka kama a Abuja, ya kasance jami’an tsaro na nemansa kan ayyukan garkuwa da mutane a Babban Birnin Tarayya Abuja da kuma Jihar Kogi.
- An kama matar ɗan ta’adda Ado Aliero da mahaifiyarsa a cikin maniyyata a Saudiyya
- An cimma matsaya kan dakatar da haska fina-finai 22 a Kano
- Yadda Boko Haram ta kashe manoma 90 a Borno cikin wata 5
Wani babban jami’in tsaro a Sakkwato ya shaida wa wakilinmu cewa ana yi wa Sani Galadi tambayoyi kuma yana ba da muhimman bayanai kafin a gurfanar da shi a kotu.
Gane da tambayar da wakilin namu ya yi masa kan yadda aka yi dan bindigar ya samu tantancewa domin zuwa aikin Hajji, sai jami’in ya sanda da cewa, “sai ka tambayi hukumomin da abin ya shafa.”