✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

An kama yaro mai shekara 14 a cikin ’yan bindigar Katsina

Yaron ya ce ya kashe mutane kuma ya iya sarrafa bindiga kirar AK 47.

Jami’an tsaro sun kama wani yaro mai shekara 14 a cikin ’yan bindiga da dubunsu ta cika a Karamar Hukumar Jibia ta Jihar Katsina.

Rundunar ’Yan Sanda ta Jihar Katsina ta gabatar da yaron ne bayan ’yan banga sun taimaka aka kama shi kan ayyukan ’yan bindiga da satar shanu a yankinsu.

Yaron wanda dubunsa ta cika a ranar 12 ga watan Oktoba,  2021, ya shaida wa ’yan sanda masu bincike cewa ya iya sarrafara bindiga kirar AK 47, kuma da shi aka kai wasu hare-haren ’yan bindga a yankinsu da ke Karamar Hukumar Jibia ta Jihar.

Da yake gabatar da yaron da sauran ’yan bindigar da suka shiga hannu, kakakin ’yan sandan jihar Katsina, SP Gambo Isah, ya shaida wa ’yan jarida cewa yaron ya amsa cewa ya taba kashe mutum biyu a wani hari da gungunsu ya kai.