‘Yan Sandan Rundunar IRT da ke aiki a karkashin Mataimakin Kwamishina Abba Kyari sun damke wasu ‘yan uwa su uku bisa zargin garkuwa da wata mata tare da hallaka ta.
Jami’an rundunar sun ce wadanda ake zargin sun bukaci kudin fansa Naira miliyan biyar daga dangin matar kafin su hallaka ta.
Mai Magana Yawun Rundunar ‘Yan Sandan Najeriya DCP Frank Mba ya ce a ranar a 14 ga watan Mayu, 2020. ne wadanda ake zargin suka kashe matar mai suna Janet Nnenna Ogbonnaya bayan sun yi garkuwa da ita a Abuja.
Mba ya ce, “Dan matar Chinedu Ogbonnaya ya kai koke ofishin ‘yan sanda cewa an yi garkuwa da mahaifiyarsa mai suna Janet Nnenna, mai shekaru 55, kana wadanda suka yi garkuwa da ita sun nemi a ba su kudin fansa Naira 5,000,000.
- Asirin budurwar da saurayi ya yi garkuwa da ita ya tonu
- Za a rataye wanda ya kashe ’yar shekara 3 ta hanyar fyade
- Kotu ta daure saurayi da budurwarsa kan satar kaji
“Hakan ce ta sa jami’an rundunar dukufa da binciken da ya yi sanadiyar kame wadanda ake zargin su uku a maboyarsu a jihar Imo, inda suka ce sun riga sun kashe ta sun binne.
“Matar ‘yar asalin jihar Abia, wadda mijinta ya rasu ta hadu da madugun wadanda ake zargin, Johnson Emmanuel, ta Facebook inda suke abota, shi kuma ya yaudare ta, ta baro gidanta da ke Gwagwalada a Abuja ta ziyarce shi.
“A nan ne ya ba ta madarar yugot wadda ya sanya kwaya a ciki, ya kashe ta, ya sa gwarta a wani ramin ajiyar ruwa na karkashin kasa, ya kuma yi amfani da wayarta ya kira danginta ya nemi su ba shi kudin fansa naira miliyan biyar kafin ya sake ta” inji Frank Mba.
A ranar Alhamis, 4 ga watan Yuni wanda ake zargin ya kai ‘yan sanda ramin da ya jefa gawar matar bayan ya kashe ta, a yankin Wumba, Lokogoma da ke Abuja inda aka hako gawar matar.
“An kai gawar Asibitin Koyarwa na Jami’ar Abuja domin ci gaba da gudanar da bincike.
“Yan sanda sun kuma gano motar Janet kirar Jeep a wani garejin gyran mota a Apo an sauya mata fenti da takardu zuwa mallakar daya daga cikin wadanda ake zargi, Johnson Emmanuel.
“Bincike ya nuna cewa gidan da aka yi garkuwa da matar aka kuma kashe ta mallakar daya daga cikinsu ne, amma suka yi gaggawar sayar da shi, domin su badda sawu, kada a gano su” inji shi.
Frank Mba ya ce Shugaban ‘Yan Sandan Najeriya ya jinjina wa jami’an da suka bankado masu laifin, sannan yi kira ga jama’a da su rika lura suna kuma ankarar da jami’an rundunar a duk sadda suka ga wani abu da basu yarda da shi ba.