✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

An kama ’yan sandan da suka yi wa budurwa kwace

Bidiyon kwacen kudin da hafsoshin ’yan sandan suka yi wa budurwar ya baza gari

Wasu hafsoshin ’yan sanda masu mukamin Isfekta sun shiga hannu bayan sun yi wa wata yarinya barazana tare da yi mata kwacen kudi.

Rundunar ’Yan Sandan Jihar Legas te ce ta kama jami’an nata su hudu ne bayan yaduwar bidiyon yadda suka yi wa budurwar kwacen mata N70,000 ne a NGAB Junction da ke unguwar Isheri a Jihar.

“Hotunan baragurnin jami’an sun karade shafukan sada zumunta, lamarin da ya sa daga Sashen Kai Daukin Gaggawa daga Abuja aka fara bincike don daukar mataki.

“Da aka titsiye jami’an, sun amsa aikata laifin tare da alkawarin za su mayar mata da kudin, wanda hakan ya isa zama hujja a kansu,” inji Kwamishinan ’Yan Sandan Jihar, Hakeem Odumosu, ta bakin kakarin Rundunar, CSP Olumuyiwa Adejobi.

Kwamishinan ’Yan Sandan ya ci gaba da cewa, “Na sa a hukunta su nan take domin ya zama izina ga sauran miyagu daga cikin jami’an Rundunar ko ma a kasa baki daya.”

Odumosu ya ce Rundunar za ta baza komarta wajen sanya kafar wando da baragurnin jami’an ’yan sanda a Jihar ta Legas.

Ya kara da cewa Runduanr na kokarin samar da kyakkyawar alaka da fahimta da yarda tsakanin Rundunar da kuma al’umma a Jihar.