Wasu ‘yan sanda biyu na tsare bayan sun yin harbin da yayi sanadiyar mutuwar wata budurwa ‘yar shekara 17.
Kwamishinan ‘yan sandan Jihar Legas Hakeem Odumosu ya ce ana binciken jami”an masu mukamin ASP da Isfekta domin gurfanar da su.
Da yake ta’aziya ga iyalan marigayiyar kwamishinan ya bukaci jama’a su kwantar da hankali domin ana ci gaba da tsare mutanen.
Kakakin Rundunar DSP Bala Elkana ya shaida wa Aminiya cewa Kwamishinan ya umarci a zurfafa binciken musababbin kisan Tina Ezekwe.
- Za a biya masu sharan kwata albashin N20,000
- Yanzu-yanzu: Tsohon Shugaban NNPC Maikanti Baru ya rasu
- Babu wani sabon hari da aka kai a Kajuru – Shugaban Karamar Hukuma
“Yan sandan da ake zargi da yin harbin na tsare ana ci gaba da bincike kafin a gurfanar da su a gaban kotu
“Sun hadar da ASP Theophilus Otobo da Isfekto Oguntoba Olamigoke masu aiki a caji ofis din Bariga.
“A ranar 26 ga watan Mayun 2020 a yankin Berger Yanaworu wadanda ake zargin suka yi harbi.
“Ya jikkata wani Musa Yakubu, harsashi ya sami budurwar a cinya ya yi sanadiyar mutuwar ta,” in ji shi.
DSP Bala Elkana ya ce ba a san dalilin harbin ba. An kai budurwar asibiti amma ta mutu bayan kwana biyu.
“Rundunar na takaicin lamarin, muna kuma ci gaba da tuntubar iyalin marigayiyar.
“Jama’a su kwantar da hankali domin muna yin duk abun da ya kamata a kan lamarin,” inji shi.
Yace rundunar zata ci gaba da sanar da al’umma halin da ake ciki game da lamarin.