Rundunar Sojin Najeriya ta samu nasarar kame wasu mayakan kungiyar Boko Haram biyu a yankin Muna da ke Jihar Borno.
Dubun ’yan ta’addan ta cika yayin wani simame da dakarun batalaiya ta 195 karkashin rundunar Operation Hadin Kai suka gudanar tare da hadin gwiwar rundunar sa kai ta farin kaya wato Civilian JTF.
- ’Yan fashi sun harbe wani hafsan soja a Jigawa
- Buhari ya umarci a gaggauta ceto duk daliban da aka sace
Hakan na kunshe cikin wata sanarwa da Darektan Hulda da Al’umma na rundunar sojin, Birgediya-Janar Onyema Nwachukwu ya fitar a ranar Talata.
“Dakarun da suka fita aikin sintiri sun kai wa wasu ’yan ta’adda simame a kauyen Labe, wadanda suka yi yunkurin tserewa amma aka cimma su cikin hanzari,” a cewar sanarwar.
A cewarsa, dakarun da suka karade yankin baki daya, sun kuma tarwatsa dukkan sansanonin da aka gano na ’yan ta’addan ne.
Birgediya Onyema ya ce a yayin simamen ne kuma dakarun suka samu nasarar karbe wasu kayayyaki da ake shirin kai wa ’yan ta’addan.
Daga cikin kayayyakin da aka kwace kamar yadda Janar Onyema ya sanar akwai mota daya, kekuna biyar, wayoyin salula biyu, fetur, da kuma bakin mai.
Kamfanin Dillancin Labarai na Najeriya NAN ya ruwaito cewa, an kuma karbe magunguna da suka hada da na kara karfin maza, maganin kwari da na gusar da hankali da kayyayakin abinci da sauransu.
“Babban Hafsan Sojin Kasa, Manjo Janar Faruk Yahaya, ya jinjina wa bajintar da sojojin suka nuna.
“Ya kuma yi kira gare su da su dore a kan aikin domin matsantawa don ganin sun kwato dukkan yankunan da ’yan ta’addan suka mamaye.”