’Yan sanda sun kama ’yan bindiga guda biyar bayan musayar wuta da su a Yankin Babban Birnin Tarayya.
An kwato bindigogi kirar AK-47 da wata kuma a hannun ’yan bindigar da aka kama a dajin da ke tsakanin yankin Gwagwa Dei-Dei da ke wajen garin Abuja.
Kwamishinan ’Yan Sandan Abuja, Benneth Igweh, ya sanar a safiyar Alhamis cewa ’yan bindigar sun shiga hannu ne a samamen kwana uku da rundunar ta gudanar a yankin.
Ya ce bayan samun bayanai kan ayyukan bata-garin ne ’yan sanda suka yi dirar mikiya a maboyar ’yan bindigar, inda bayan musayar wuta suka kamo su kan garkuwar da aka yi da mutane ranar 12 ga watan Yuni, 2024.
- Makamai da kwayar N13.9bn muka kama a Ribas —Kwastam
- Tela Maize: Binciken fasasha ya samar sabon irin masara mara illa —Jami’ar ABU
Ana zargin sun karbi kudin fansa miliyan N12 daga iyalan wasu daga cikin mutanen da suka sace, duk da cewa masu garkuwar sun kashe biyu daga cikin mutanen da suka sace.
A cewar Igwe, ’yan bindigar, wadanda duk matasa ne sun amsa laifin da ake zargin su na addabar yankin da sace mutane domin karbar kudin fansa.
CP Igweh, ya ce da zarar rundunarsa ta kammala bincike za ta gurfanar da su a kotu domin su girbi sakamakon abin da suka shuka.
Sannan ya ba wa jama’a tabbacin yin aiki tukuru domin tabbatar da tsaron rayuka da dukiyoyin al’ummar.
Daga nan ya ja hankalinsu da su kasance masu lura tare da kiran wadannan lambobin kar-ta-kwana a duk lokacin da bukatar hakan ya taso: 08032003913, 08028940883, 08061581938, and 07057337653.