Rundunar ’yan sandan Nijeriya ta kama wata mata, Hauwa Yusuf mai shekara 30 da makamai a hanyar Abuja zuwa Kaduna.
Rundunar ta ce jami’anta na musamman sun cafke matar wadda ta boye bindiga kirar AK47 da ƙwanso huɗu na harsashin bindigar a cikin buhun garin kwaki.
- Ambaliyar ruwa ta rusa gadar da ta haɗa garuruwa 5 a Kebbi
- ’Yan bindiga sun saki malamin da suka sace a Zariya
Kakakin rundunar, Muyiwa Adejobi ne ya bayyana hakan a cikin birnin Abuja a ranar Juma’a yayin da yake shaida wa manem labarai kwazon da rundunar ta yi tsawon wata guda da ya gabata.
Adejobi ya ce an kama matar ce a lokacin binciken ababen hawa a kan babbar hanyar Abuja zuwa Kaduna.
Kakakin ya kara da cewa matar, ta fada da bakinta cewa wani dan fashin daji da ya yi kaurin suna, wanda ke addabar al’ummar Jihar Katsina mai suna Aminu Basullube, shi ne ya aike ta kai makaman wani sansani na Danum Madam da ke jihar.
Adejobi ya ce a ranar Laraba ce aka kama matar, wadda ta gaya wa manema labarai cewa ba ta san da makamai ba a buhun da aka ba ta saƙo ta kai.
Sai dai matar wadda ta taso daga birnin Lafiya na Jihar Nasarawa, ta ce an ba ta naira 130,000 ta kai saƙon Jihar Katsina.
Kakakin ’yan sandan ya ƙara da cewa, a tsawon wata guda da ya gabata, rundunar ta samu nasarar cafke mutum 2,726 da ake zargi da aikata miyagun laifuka.
Kazalika, ya ce rundunar ta samu nasarar kuɓutar da mutum 207 da aka yi garkuwa da su tare da kwato makamai da alburusai aƙalla 2,000 a tsawon lokacin.