✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

An kama wasu dauke da makamai a Binuwe

Rundunar sojojin Najeriya ta kame gungun mutum tara dauke da bindigogi kirar AK47 a jihar Taraba wadanda ake zargin gwamnatin Binuwe ce ta dauke su…

Rundunar sojojin Najeriya ta kame gungun mutum tara dauke da bindigogi kirar AK47 a jihar Taraba wadanda ake zargin gwamnatin Binuwe ce ta dauke su aiki tare da basu makamai.
 
Nasarar da rundunar sojan ta samu na kame mutanen ta zo daidai da lokacin da jihohin da ke makwabtaka da juna ke cikin tashin hankalin fadan fulani makiyaya da manoma inda rayuka kusan 100 suka salwanta a cikin kwanaki bakwan farko.
 
Kama mutanen ya bude sabon babi wajen kokarin da ake yi na kawo karshen tashe-tashen hankulan da suke nema su gagari kwandila.