✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

An kama wani ɗauke da ƙoƙon kan mutum a Ogun

Rundunar ’yan sanda a Jihar Ogun ta yi nasarar kama wani mutum ɗauke da ƙoƙon kan mutum a buhu, a cewar Kakakin rundunar, ASP Abimbola…

Rundunar ’yan sanda a Jihar Ogun ta yi nasarar kama wani mutum ɗauke da ƙoƙon kan mutum a buhu, a cewar Kakakin rundunar, ASP Abimbola Oyeyemi.

Rundunar ta yi nasarar kama mutumin mai suna Babalola Aled ɗan shekara 25, a sakamakon bayanan sirri da ta samu. “Su biyu ne ke tafe da buhun ɗauke da kan mutum, koda jami’anmu suka far masu sai ɗayan ya tsere,” inji shi.

Wanda ake zargin ya shaida cewa wani boka ne ya umarce su da su kawo masa ƙoƙon kan mutum da nufin yi masu maganin kuɗi.

Kwamishinan ’yan sanda a Jihar Ogun, Ahmad Iliyasu ya shaida wa Aminiya cewa ko kaɗan rundunar ba za ta raga wa ɓata gari a jihar ba. Don haka rundunar na kan neman wanda ya tsare kuma za a gurfanar da wanda aka kama da zarar an kammala bincike a kansa.

A ’yan kwanakin nan ana samun yawaitar ɓata garin da ke safarar sassan jikin mutum, domin neman abin duniya. Ko a kwanakin baya ma a garin Sabo-Abekuta, al’ummar Hausawan garin sun ga alamar an tona ƙaburbura biyu a maƙabartarsu, inda ake zargin wasu miyagu ne ke ƙetarawa cikin maƙabartar, suna haƙar kaburbura.