✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

An kama wanda ya yi yunkurin sace Bature a Zariya

‘Yan sanda sun kama wani da ake zargi da sace mutumin China domin nema kudin fansa a Zariya. Wanda ake zargin dan asalin Jihar Kuros…

Yan sanda sun kama wani da ake zargi da sace mutumin China domin nema kudin fansa a Zariya. Wanda ake zargin dan asalin Jihar Kuros Ribas mai suna Paul Ochala tsohon ma’aikaci ne a kamfanin da ya yi aikin samar da ruwa na garin Zariya wato CGC, kuma yana zaune ne a Unguwar Mugu da ke Dakace a hanyar Jos.

Wakilinmu ya ga cincirindon mutanen da suka yi wa mai satar Baturen a ture, lokacin da suka farga yana gudun fitar hankali da wata mota kirar Hilos, mai dauke da tambarin CGC, yana kokarin tserewa da wanda ya sato mai suna Zhang Ligun dan kasar China.

Mataimakin Kwamishinan ’Yan sanda mai kula da Shiyya ta Daya da ke Zariya, Abdullahi Ibrahim da DPO din Zariya da na Tudun Wada da suka halarci wurin da aka kama wanda ake zargin su suka dauki Baturen zuwa harabar kamfain CGC da ke Dakace.

Shugaban ’yan sandan wanda ya tara Turawan da ke aikin samar da ruwa na Zariya ya gargade su cewa su daina fita ba tare da jami’an tsaron da aka tanada domin su ba, ya ce inda za su fita su tabbatar sun dauki jami’in tsaro.

Ya bukaci jama’a su ci gaba da taimaka wa jami’an tsaro wajen kula da duk wani abu da ba su gane masa ba.

Da wakilinmu ya nemi jin karin bayani daga shugaban ’yan sandan ya ce “Abin da kake gani ke nan da idanunka, ya saci Bature ne yana neman yin garkuwa da shi domin neman kudi sai Allah Ya sa muka kama shi, kuma mun same shi da bindiga karama kirar gida. Dama mako biyu da suka wuce mun kama ’yan uwansa da aka kore su daga aiki tare, wadanda dukansu tsofaffin ma’aikata ne a kamfanin aikin samar da ruwa na Zariya. An same su suna bin kayayyakin da ake harhadawa na aikin ruwa suna kwakwancewa, kuma sauran da suka fito daga Jihar Akwa Ibom, suna hedikwatarmu ana bincike a kansu.” 

Direban Baturen mai suna Muhammadu ya shaida wa Aminiya cewa, “A ranar Litinin da misalin karfe 11:30 na safe na dauko mai gidana  za mu duba aiki sai na ga wadansu mutum biyu sun tsare mu da bindiga, suka ciro ni daga motar suka jefar a gona, suka gudu da motar da mai gidana. Sai na tashi na bi su a guje ina ihu, amma suka yi min nisa. Daga baya Allah Ya sa aka kama su kuma wanda aka kama tsohon ma’aikacin gidan ne mai suna Paul Ochala wanda aka kora.”

Kakakin Rundunar ’Yan sandan Jihar Kaduna, ASP Yakubu A. Sabo ya tabbatar da faruwa lamarin inda ya ce wanda aka kama tsohon ma’aikacin kamfanin CGC ne kuma dalilin zarginsu da rashin gaskiya aka kore su. Ya ce za su ci gaba da bincike har sai sun gano sauran abokan ta’asarsa, inda ya yaba wa jama’a kan taimakawar da suke yi wajen kula da abin da ke kai da komo.