Dakarun bataliya ta 152 ta ‘Operation Hadin Kai’ a Banki, sun kama wani tubabben dan ta’addan Boko Haram, Ba’ana Bdiya wanda aka fi sani da “Manci” wanda ya kitsa kai wa sojoji hare-hare a Jihar Borno.
Wannan dai na zuwa ne kasa da mako guda bayan da wasu tsoffin tsageru biyu, Goni Farouq da Amir Zabu, wadanda su ne manyan tsoffin kwamandojin Boko Haram, da suka shiga wata tattaunawa ta wayar tarho, inda suka shirya kai hari kan sojoji.
- Majalisa za ta binciki musabbabin yawan hatsarin jirgin kasa a Najeriya
- Ba mu gamsu da zaben Bauchi ba, kotu za mu tafi – APC
Ba’ana yana cikin dubban ‘yan Boko Haram da suka ajiye makamansu kuma al’umma ta karbe su, amma duk da zubar da makamansa ya ci gaba da yin alaka da abokan ta’addancinsa na baya.
Wata majiyar leken asiri ta shaida wa Zagazola Makama, kwararre kan yaki da tada kayar baya kuma mai sharhi kan harkokin tsaro a yankin Tafkin Chadi, cewa bayanan da Ba’ana ya bayar sun taimaka wa ‘yan Boko Haram wajen samun nasarar yi wa sojoji kwanton bauna a lokacin da suke sintiri a Ngauri wanda ya kai ga kashe wasu sojoji a watan Fabrairu 2023.
A ranar 16 ga Maris, 2023, wanda ake zargin ya ba da wani bayani game da zirga-zirgar dakaru wanda ya bai wa ‘yan ta’adda damar kai musu hari har aka kashe sojoji uku tare da jikkata wasu hudu a bayan garin Banki.
Majiyar ta koka da cewa wani lokaci sojoji ke samu wajen kokarin kawar da ‘yan ta’addar Boko Hama gaba daya, shi ne munanan ayyukan ‘yan rahoto na cikin gida irin su Ba’ana.
Akwai damuwa cewa ci gaba da sakin ‘yan ta’addan da suka tuba cikin al’umma ba tare da tsangwama ba na iya kawo nakaso wajen ci gaban da ake samu kawo yanzu a yakin da ake da ‘yan tawayen na Boko Haram da na ISWAP.
Akwai bukatar a yi amfani da tsarin gyaran fuska da yawa na tsoffin mayaka.
Bayan wannan, akwai kuma bukatar gwamnatin tarayya ta taimaka wa sojoji da gwamnatin jih6ar Borno wajen lalubo hanyar da za a bi wajen tunkarar tsoffin ‘yan bindiga sama da 90,000 da suka mika wuya tare da watsar da akidarsu ta tada kayar baya.