✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

An kama wanda ya kitsa harin jirgin kasan Abuja-Kaduna

An kuma sani tsabar kudi a hannun mutumin

Rundunar Sojin Najeriya  ta kama wani mutum da ake zargi shi ne ya shirya harin jirgin kasan Kaduna zuwa Abuja na ranar 28 ga watan Maris 28, 2022.

Daraktan yada labaran rundunar ta musamman, Manjo Janar Musa Danmadami ne ya bayyana hakan a Abuja ranar Alhamis, inda ya ce daga cikin kudaden da aka samu wanda ake zargin, har da Dala 5,000.

Danmadami ya ce mutunin ne cikon na uku daga mutanen da rundunar ta kamo  a kauyen Damba da ke Karamar Hukumar a ranar 14 ga watan Fabrairu.

Ya kuma ce a yayin wani sumame da suka gudanar ne suka gano babura biyu da wayoyin hannu mallakin wadanda ake zargin.

Haka kuma a wani sumamen da suka gudanar Unguwar Birni da ke Karamar Hukumar Kajuru, sun gano harsasai da dama, da manyan bindigu guda bakwai, da sauran kayayyaki, mallakin wadanda ake zargin.