Sojojio sun kama masu hada baki da ’yan bindiga da masu ba su bayanai a harin da suka kai har suka kashe soja 15 a Jihar Sakkwato.
Da yake bayani kan kamen da dakarun rundunar Operation Hadarin Daji suka yi, kakakin Hedikwatar Tsaro, Birgediya Benard Onyeuko, ya ce bayan harin, sojoji sun tsananta kai wa ’yan bindiga hare-hare suna ragargazar su a yankin Arewa maso Yamma.
- Zargin batanci: Kotu ta hana Abduljabbar beli
- Najeriya A Yau: Yadda Zamfarawa ke rayuwa cikin damuwa
Birgediya Onyeuko ya ce hare-haren sun karya lagon bata-garin, sun kuma hana su motsi, ballanta samun makamai ko kayan da aka haramta ko su kai hari, gami da ba wa mazauna yankin kwarin gwiwa.
Idan ba a manta ba mun kawo rahoton harin ’yan bindiga da suka hallaka sojoji da sauran jami’an tsaro da dama a wani sansanin soji a Karamar Hukumar Sabon Birni ta Jihar Sakkwato.
Onyeuko ya ce, “Sauran sun hada da harin da aka kai sansanin sojin da ke garin Burkusuma da kauyen Makuwana a Karamar Hukumar Sabon Birni ta Jihar Sakkwato, da garin Sabuwa na Jihar Katsina inda aka tare hanyar Gimi zuwa Gora.
“Martanin da sojoji suka mayar da manyan makamai cikin gaggawa ya sa ’yan bindigar tserewa, aka kuma kama wasu, ciki har da masu kai musu bayanai da masu taimaka musu”.
Onyeuko ya bayan makamai da sauran abubuwa da aka kama a hannun ’yan bindigar, daillalin makamai da masu kai musu bayanai sun shiga hannu a kauyen Kofar Fada da ke Karamar Hukumar Kankara, da kauyen Shabba na Karamar Hukumar Jibiya sai kuma kayukan Kaiga da Ummandau da Gammu, duk a Jihar Katsina.