Mutum biyu da ake zargi da kisan wani matashin matukin jirgin sama, Kyaftin Abdulkareem, babban dan Sanata Bala Ibn Na’Allah, sun shiga hannu.
Majiyoyinmu sun ce an kama mutanen ne a ’yan kwanakin da suka wuce, bayan kisan gilla da aka yi wa matashin mai shekara 36 a gidansa aka kuma yi awon gaba da motarsa.
- An kashe ’yan Najeriya 693, an sace 494 a watan Agusta —Rahoto
- Yadda kashe Al-Barnawi ka iya karya lagon mahara a Najeriya
Da yake tabbatar da kama wadanda ake zargin, Jami’in Hulda da Jama’a na Rundunar ’Yan Sanda Jihar Kaduna, ASP Jalige Mohammed, ya ce, “Gaskiya ne mutum biyu daga cikin wadanda ake zargi sun kashe Abdulkareem Na’Allah suna hannunmu. Daya kuma ya tsere”.
Babu cikakken bayani game da wadanda ake zargin da suka shiga hannu, amma majiyarmu ta ce matasa ne masu shekara 20 da wani abu.
Majiyar ta ce an kuma gano motar mamacin, wadda maharan da suka kashe shi suka yi awon gaba da ita a kan iyakar Jamhuriyar Nijar.
A ranar 29 ga watan Agusta ne aka yi wa matashin matukin jirgin saman kisan gilla a gidansa da ke unguwar Malali GRA a garin Kaduna.
Mahaifin Abdulkareem dai shi ne Sanata mai wakiltar Kebbi da Kudu a Majalisar Dattawa.