Wadansu ’yan bindiga sun sace dan shahararren dan siyasar nan Alhaji Bashir Bukar Rimin Zayam da wata budurwa ’yar Shugaban Jam’iyyar APC na Karamar Hukumar Toro a Jihar Bauchi Alhaji Sha’aban mako uku kafin aurenta.
Kakakin ’Yan sandan Jihar Bauchi DSP Kamal Datti Abubakar ya tabbatar da sace mutanen biyu, inda ya ce tuni an sako su kuma an kama mutum biyar da ake zargi.
Da yake bayani ga manema labarai a madadin iyayen yaran, Alhaji Bashir Bukar Rimin Zayam ya ce suna godiya ga Allah da kuma ’yan uwa da abokan arziki da gwamnati da rundunar ’yan sanda da dukan wadanda suka taimaka aka sako ’ya’yansu.
Wani makwabcinsa a garin Rimin Zayam da bai so a ambaci sunansa ya ce abin ya faru ne da misalin karfe 1:00 na dare lokacin da ’yan bidigan suka je gidan Alhaji Bashir din suka yi kokarin karya kofa da ta gagara sai suka zaga ta baya suka haye ta katanga suka shiga har cikin iyalinsa suna nemansa. Ya ce da aka ce musu ya yi tafiya, sai suka bincike gidan daki-daki suka dauki kayayyaki, suka kwace wayoyin hannu, sannan suka sace yaron suka tafi da shi suka ce ya nuna musu lambar babansa a cikin wayar.
Ya ce da suka fito kuma sai suka shiga gidan Shugaban APC na karamar hukumar suka dauki ’yarsa budurwa, wadda saura mako uku aurenta suka tafi da su.
Ya ce daga nan aka yi ta kokarin tattaunawa da su ana ciniki har Allah Ya ba da nasara suka zo suka ajiye su a bayan gari su kuma suka karaso gida.
Ya yaba wa ’yan sandan jihar bisa namijin kokarin da suka yi, sannan ya bukaci ssu tabbatar an hukunta wadanda suka aikata wannan mugun aiki, tare da bincikarsu har sai sun fadi wanda ya turo su.