’Yan sandan sun cafke wata mata, mai shekara 21 a duniya, bisa zargin sayar da jaririnta mai wata uku a haihuwa a kan N150,000.
Kakakin ’yan sandan Jihar Anambra, inda aka kama matar ya ce wadda aka zargin ta fito daga kauyen Ire-Ojoto na Jihar Akwa Ibom.
- Fitila ta kona jariri kwana daya da haihuwarsa
- An sace jariri bayan kwana uku da haihuwa
- An cafke mata bisa zargin satar jariri dan wata 6
- Mai jego da jariri sun kubuta daga hannun ’yan bindiga
“Bayan gudanar da bincike an gano matar ta yi yunkurin sayar da jaririn mai wata uku a duniya nesaboda shiga matsanancin hali da ta yi.
“An ceto jaririn kuma yana cikin koshin lafiya, za a ci gaba da bincike don gano dalilinta na yin haka”, cewar Haruna.
Wannan ba shi ne karon farko da aka samu uwa na shirin sayar da jaririn da ta haifa ba.
Wasu na fakewa da cewa talauci da wahalar rayuwa ce ke tilasta su yin hakan.